Jirgin Kasa Ya Halaka Mutane a India

Wani jirgin kasa a yankin Amritsar ya halaka mutane akalla 60 inda kuma ya raunata wasu akalla 100 a yayin da yayi kutse a cikin wasu masu taro a arewacin yankin Punjab.

Su dai wadanda hatsarin ya rutsa dasu suna tsaye ne akan digar jirgin inda suke bikin Dusshera wanda aka sabayi a kasar ta India domin tunawa da wani abu da ya faru mai kyau ko marar kyau.

Yara da dama suna cikin wadanda hatsarin ya rutsa dasu.

Wani wanda abin ya faru a gaban sa ya shaidawa manema labarai cewar mutane da dama suna ta shagali yayin da wasu suke ta daukar hotuna da wayoyin su na tafi da gidan ka inda jirgin ya iske ku a guje.

Shi dai jirgin da yayi wannan kutse yana kan hanyar sa ne daga garin Jalandhar izuwa Amritsar.

183total visits,1visits today


Karanta:  Fyade: 'Yar shekara goma ta haihu a India

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.