Jirgin sojin sama ya yi ragargaza a maboyar ‘yan boko haram

Rundunar sojojin sama ta Najeriya ta bada sanarwar cewar jiragenta sun yi ragargaza akan wasu maboyar ‘yan kungiyar Boko Haram dake cikin dajin Sambisa.

Mai magana da yawun rundunar, Kwamanda Olatokunbo Adesanya ya bayyana hakan a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta na 2017. Ya kara da cewa rundunar mayakan sama ta cikin shirin ‘Operation Lafiya Dole’ sun gudanar da wani binciken sirri a yankin Parisu, dake cikin dajin Sambisan. A yayin wannan bincike ne aka gano wasu gungun taron ‘Yan kungiyar ta Boko Haram na taruwa a wata maboya dake karkashin wata bishiya wadda aka kare da rufin kwano, yanayin da zai sa ba za a gane cewar wata maboya bace a fakaice.

Tabbatattun bayanai na sirri sun nuna cewar, lallai wannan waje maboya ce ta ‘Yan kungiyar Boko Haram wadda ta kunshi mafakarsu da wajen kwanansu.

Kwamanda Adesanya ya kara da cewar a ranar 8 ga Agusta 2017, aka bada umarni ga jirgin yaki da ya ragargaza wannan wuri ba tare da kakkautawa ba.

“A hari na farko da na biyu aka ragargaza ginin da sauran abubuwan da ke zagaye da shi, a yayin da a hari na uku aka wargaje wajen gaba dayansa sai fili” in ji Adesanya.

 

 

Asalin Labari:

DailyTrust, Muryar Arewa

477total visits,1visits today


Karanta:  An kama ''yan luwadi 42' a Legos

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.