Justin Bieber ya samu kutsawa cikin jerin masu kudin London

Shahararren mawaki nan da aka sani da Justin Bieber ya samu kansa a wani jerin gwanon masu kudi a garin London dake kasar Birtaniya.

A wani rahoto ta sashin Mansion Global ya wallafa ya nuna cewar masu kudi mazauna arewacin London suna kusa da samun kansu a cikin bacin rai sakamakon shigar matashin mawaki Justin Bieber izuwa wani katafaren gida dake a wannan unguwa inda ya yi hayar wani gida akan kudi Naira milliyan 48 (£108,000) a kowanne wata a wani layi a akewa lakabi da “The Bishops Avenue” a cikin unguwar Hampstead.

Masu hasashe dai sunyi ittifaki da cewar Bieber zai dan dade a wannan gida sakamakon raba wajen zama da yake so yayi a tsakanin mazauninsa dake garin Califonia da kuma garin na London.

Rahoton ya kara da cewa wannan mazauni zaiyi kyau da Bieber, dan shekara 22, inda zai samu damar kebancewa tare da masoyansa. Shi dai wannan gida yana zaune ne akan eka 2.5 na fili inda yake da falo har kala shida, filin buga kwallon hannu da kuma dakin wanka na ciki dana waje baki daya.

Bugu da kari, a cikin gidan na Bieber a akwai dakin katafaren dakin kallo sai dakin gasa jiki da kuma wajen shakatawa, inda ya hada da wajen ajiye motoci kimanin guda hamsin da kuma dakin kota kwana.

1897total visits,1visits today


Karanta:  An hana ni aure saboda zargin luwadi - Adam A Zango

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.