Ka san illolin kaifin basira kuwa?

Kana jin basira za ta iya kasancewa matsala mai ban takaici maimakon alheri mai tarin amfani? Watakila ka amince da haka ko kuma ka kekasa kasa ka ce ba ka yarda da wannan magana ba, ko?

Yi nazarin wannan binciken da David Robson ya yi wa BBC

Idan jahilci alheri ne, ko basira za ta iya zama masifa? Yawancin mutane za su ce haka abin yake.

Muna daukar mutanen da suke da baiwa a matsayin wadanda suke tattare da wata damuwa da kadaici.

Ka duba mutane irin su Virginia Woolf da Alan Turing ko Lisa Simpson dukkaninsu za ka ga sun yi fama da kadaici, ko da a lokacin da suke kan ganiyarsu.

Kamar yadda Ernest Hemingway ya rubuta: ”Farin ciki a wurin masu basira abu ne da ba kasafai ba wanda na sani.”

Za a iya ganin wannan magana kamar wani karamin abu ne da ya shafi wasu mutane ‘yan kadan, amma hasken da take bayarwa abu ne da zai iya shafar mutane da yawa.

Yawancin manufofinmu na ilimi sun bayar da fifiko ne wajen bunkasa abin da ya shafi boko ko wanda ake koyarwa a makaranta.

Duk da cewa an san yana da iyaka amma har yanzu ana amfani da ma’aunin kaifin basira (IQ) a matsayin hanyar auna basirar mutum, kuma muna kashe makudan kudade wajen horad da kwakwalwa da bunkasa ta domin cimma wannan mataki na yawan maki na ma’aunin kaifin basira.

To amma kuma ina amfanin badi ba rai, idan duk bayan wannan dawainiya abin da za a samu (kaifin basira) ba shi da wani amfani?

Kimanin shekaru dari daya da suka gabata ne aka dauki matakin farko na amsa wannan tambaya, a lokacin ganiyar kidan Jazz na Amurka.

A wannan lokacin sabon tsarin jarraba kaifin basira na tashe, bayan da aka ga tasiri da muhimmancinsa a cibiyoyin daukar soji na yakin duniya na biyu, da kuma yadda Lewis Terman ya yi amfani da tsarin wajen ganowa da kuma nazari a kan wasu yara ‘yan baiwa.

Karanta:  Yadda aka kama masu cin naman mutane a Afirka Ta Kudu

A lokacin ya bincike makarantun California na yaran da suka fi kokari, inda ya zabo 1,500 wadanda ma’aunin basirarsu ya kai lamba 140 ko sama da haka.

Haka kuma daga cikinsu akwai wadanda nasu ya wuce lamba 170.

Da aka hada gaba dayansu ne sai aka kira su da Ingilishi ”Termites” (Gara), kuma har zuwa yau ana nazarin rayuwarsu.

Kamar yadda na san za ka yi tsammani, yawancin wadannan yara ko dalibai (Termites) sun samu dukiya da suna.

Fitacce a cikinsu shi ne Jess Oppenheimer, wanda ya rubuta wasan kwaikwayon nan na shekarun 1950 mai suna ”I Love Lucy”.

Lokacin da aka fara nuna wannan wasan kwaikwayo na shi a tashar talabijin ta CBS, albashin yawancin takwarorinsa (termites) ya linka na yawancin mai aikin ofis biyu.

To amma ba duka daga cikin wadannan dalibai ‘yan baiwa ba ne suka cimma abin da Terman ya yi tsammani ba.

Akwai wasunsu da yawa da suka zabi wasu ayyukan na daban na rufin asiri kamar, aikin dan sanda da aikin jirgin ruwa da aikin akawu.

A bisa wannan dalilin ne Terman ya ayyana cewa ”basira da cimma nasara a rayuwa ba lalle ne a ce suna da dangantaka ba”.

Ma’ana ba dole ba ne a ce mutumin da yake da basira ya samu nasarar zama wani abu a rayuwa.

Kuma ba wajibi ba ne basirarsu ta jawo musu farin ciki.

A rayuwar wasunsu (Termites) sun yi fama da matsalar mutuwar aure da shan barasa da kashe kansu.

A lokacin da suka kai shekarunsu na tsufa wadannan dalibai masu basira (Termites), an rika maimaita darasin da ke tattare da labari ko rayuwarsu.

Karanta:  An fara rububin bargo a kasuwa

Darasin kuwa shi ne, basira ba daya take da kyakkyawar rayuwa ba; ta iya ma kasancewa ba ka cimma burinka a rayuwa ba.

To amma ba wannan ba yana nufin a ce duk wanda yake da kaifin basira (IQ) ya gamu da matsala ko damuwa ba kamar yadda yawancin mutane za su dauka ba, abu ne dai da zai iya kasancewa mai rikitarwa.

Me ya sa ba za a ga amfanin kaifin basira ba a karshe?

Kaya mai nauyi

Wani abu da zai iya kasancewa shi ne ilimin basirarka zai zama kamar dabaibayi a wurinka.

A shekarun 1990, an bukaci wasu daga cikin wadannan dalibai masu kaifin basira (Termites) da su waiwayi rayuwarsu ta shekara 80 da suka yi.

Maimakon su ga irin nasarorin da suka cimma a rayuwa, da dama daga cikinsu sun nuna nadama da damuwa cewa ba su cimma abin da ya kamata su cimma ba, idan suka yi la’akari da baiwar da suke da ita a lokacin suna da kuruciya.

Tunanin irin nauyin da ke kan mutum musamman idan aka hada da irin abin da wasu ke sa rai a kanka, abu ne da ke addabar yara da yawa masu kaifin basira ko wata baiwa.

Babbar abar dubawa a irin wannan ita ce Sufiah Yusof wadda ke da baiwar lissafi, wadda aka dauke ta a Jami’ar Oxford tun tana da shekara 12, amma kuma ta yi watsi da karatun kafin ta yi jarrabawarta ta fita, kuma ta kama aiki a otal.

Daga karshe ta zama mai nishadantar da baki da baiwarta ta hanyar tilawar hanyoyin lissafi iri daban-daban yayin da take rawa ta batsa.

Karanta:  Wata tsohuwa ta kammala digiri a shekara 91

Wata matsala da ake yawan ji a wurin haduwar dalibai da tarukan intanet ita ce, mutane masu basira suna ganin irin matsaloli da gazawar duniya fiye da sauran jama’a.

Yayin da yawancinmu ba ma gani tare da damuwa da matsalolin gazawar duniya, masu kaifin basira kuwa suna cike ne da damuwa kan halin kuncin da wasu ke ciki ko kuma sakarci da wawancin da wasu mutanen ke yi.

Yawan damuwa zai iya kasancewa wata alama ta kaifin basira, amma ba kamar yadda masu falsafa ta cima-zaune suka dauka ba.

Da ya gudanar da bincike tare da tambayar dalibai a makaranta a kan abubuwa da dama na rayuwa, Alexander Penny na Jami’ar MacEwan da ke Canada ya gano cewa wadanda suke da kaifin basira suna cikin damuwa duk tsawon rana.

Kuma abin mamakin shi ne damuwar ta al’amrun duniya ne na yau da kullum.

Kuma wani abin shi ne daliban da suka fi kaifin basira sun fi nanata magana kan wani abu na damuwa da ya faru, maimakon tambaya.

” Ba wai cewa damuwarsu ta fi ta kowa ba ne, a’a, abin shi ne sun fi damuwa ne sosai a kan karin wasu abubuwan,” in ji Penney.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1190total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.