‘Kai mana hari ba zai razana mu ba’

Mukaddashin shugaban Hukumar da ke yaki da rashawa a Najeriya, EFCC, Ibrahim Magu ya ce babu abinda zai razana su dangane da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai ofishin su da ke Abuja

A tattaunawarsa da RFI Hausa, Magu, ya ce wannan hari zai dada karfafa musu gwiwa kan ayyukan da suke yi na kwato dukiyar talakawa da barayi suka yi rub da ciki a kai.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 5 na Asuban Laraba, inda suka bude wuta kan ofishin da ke unguwar Wuse, suka kuma lalata motoci kafin jami’an hukumar su kore su.

 

Kazalika Maharan Sun ajiye wasikar barazana a gini Hukumar.

Ofishin EFCC da ke Wuse ne ke da alhakin binciken laifufukan da suka shafi halarta kudaden haramun a karkashin Ishaku Sharu.

Yanzu haka dai ofishin na gudanar da bincike kan mutane da dama cikin su harda ‘yan siyasa da ake zargi da aikata irin wadanan laifufuka.

Asalin Labari:

RFI Hausa

578total visits,1visits today


Karanta:  Masu Gangamin "Mumu don Do" Na Neman A Dawo da Tsohuwar Ministan Man Fetur daga Ingila

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.