Kalaman nuna kiyayya ta’addanci ne — Osinbajo

Mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya ce gwamnati za ta fara daukar amfani da kalaman nuna kiyayya a matsayin ta'addanci, kuma ya ce gwamnati ta ja layi a kan batun daga yanzu.

Ya bayyana haka ne a lokacin taron Kwamitin Kula da Tattalin Arziki na kasa, wanda ake gudanarwa a ranar Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.

“Rashin maganar da shugabannin al’umomin kasarmu ke yi game da halin rashin tsaro a halin yanzu ya zama wani babban kalubale”.

“Rashin cewa komai game da wannan batun na iya zama tamkar amincewa ne da halin da muke ciki”, in ji mukaddashin shugaban kasar.

Ya kara da cewa dokar nan ta hana ayyukan ta’addanci ta shekarar 2011, ta ayyana ta’addanci a matsayin duk wani aiki da aka yi da kokarin muzgunawa wani ko wata da niyyar cutar da su ko cutar da Najeriya, ko wani mataki da za a iya cutar da wasu al’ummomi.

Farfesa Osinbajo ya bayar da misali da cin hancin da aka tafka a bangaren tsaro na kasar, wanda ya ce ya taimaka kwarai wajen karawa masu tayar da kayar baya karfi, inda ya ce yanzu lokaci ya yi da za a dauki mataki a aikace maimakon fashin baki a fatar baki.

“Yanzu lokaci ya yi da za mu yunkuro don aiwatar da tunaninmu da zantukanmu a kan tsaro, don ka da zancen ya bi shanun sarki.

A ranar 12 ga watan Agustan nan ne gwamnatin Najeriyar ta ce ta soma shirye-shiryen aike wa da wata bukata zuwa ga majalisar dokokin kasar da ke neman yin dokar da za ta fayyace irin hukuncin da za a yi kan wadanda aka samu suna furta kalaman kiyayya ga wani jinsi a kasar.

Gwamnati ta yanke shawarar yin hakan ne saboda yadda zaman tankiya ke karuwa tsakanin a kabilu da addinai da kuma yankunan kasar daban-daban, inda har wasu ke kiran da a raba ta ko a sake mata fasali.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1858total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.