Kallo Ya Koma Jihohi, A Yunkurin Samawa Kananan Hukumomi ‘Yanci.

Shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi komored Ibrahim khalil yace zasu addu'o'i na musamman kan wannan yaki.

 

 

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya, tace yanzu zata maida hankali kan majalisun dokokin jihohin Najeriya 36, a kokarin ganin cewa jihohin sun amince da kudurin da majalisun tarayya suka amince da shi na baiwa kananan hukumomin ‘yancin cin gashin kansu.

Shugaban kungiyar komored Ibrahim Khalil, yace ‘yan kungiyar mabiya dukkan addinai, wani lokaci nan bada jumawa ba, zasu tsaida rana ta yin addu’o’i domin Allah yayi maganin duk mutumin da zai kasance tarnaki ga yunkurin ‘yanto kananan hukumomi daga jihohi.

Karkashin tsarin, bayan da majalisun tarayya sun amince da shirin, ana bukatar jihohi 24 ko kashi 2 cikin 3 na jihohi 36 su amince da kudurin kamin wannan kokarin baiwa kananan hukumomin ya tabbata.

Shugaban reshen kungiyar a jihar Zamfara Mallam Isa Gusau, yace zasu tuntubi gwamnoni da majalisun domin kara tabbatar da musu da muhimmancin wannan kuduri a kawo ci gaban kasa baki daya.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1369total visits,1visits today


Karanta:  Osinbajo zai rantsar da sabbin ministoci 2 ranar Laraba

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.