Kamfanin Alhazai Express ya kaddamar da Manhajar Radio

Shahararren kamfanin fasaha dake jihar Kano a Nigeria, Alhazai Express, ya kaddamar da sabuwar manhajar Radio (Alhazai Radio) mai dauke da tashohin Hausa dama sauran yaruka kai tsaye a wayar tafi da gidan ka mai kirar Android.

Kamfanin ya sanar da hakan ne a shafin sa ta sada zumunta dake Twitter dama Facebook baki daya.

A cewar kamfanin wannan zai bayar da dama ga masu sauraren tashoshin Hausa da suka hada da BBC, VOA dama wadansu tashoshin Najeriya damar sauraren labarai da rahotanni cikin murya kai tsaye ba tare da amfani da tsohuwar hanyar saurare ba.

Wakilin Muryar Arewa ya tuntubi shugaban kamfanin mai suna Zubairu Dalhatu Malami inda ya bayyana masa cewar manhajar Alhazai Radio zata bayar da damar sauraren tashoshi masu yawa da suka hada da BBC Hausa dana Turanci, VOA Hausa, Express Radio, Radio Dandal Kura, Vision FM Sokoto, Aminci Radio, Liberty Kaduna da dai sauran su.

Manhajar ta Alhazai Radio wadda tuni aka dora ta akan sashin Google Play Store ta samu saukewa akalla sau dubu daya (1000 download).

5502total visits,4visits today


Karanta:  An kaddamar da sashin "Nigeria for Buhari 2019"

One Response to "Kamfanin Alhazai Express ya kaddamar da Manhajar Radio"

  1. Pingback: Kamfanin Alhazai Express ya kaddamar da Manhajar Radio | Alhazai Express

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.