Kamfanin Damfara na MMM zai dawo Hulda

Kamfanin MMM wanda aka fi sani da Mavrodi Mundial Moneybox (MMM) wanda ya karye watanni da dama a baya sun fara kokarin sabunta hajjarsu a wani sabon kuduri wanda ya nuna hakan bayan wani sabon salo da suka dauko a ‘yan kwanakin nan.

A wata wasika da kamfanin yake turawa da mambobin sa a shafin su dake kan yanar gizo-gizo, inda yake kisan su da gayyatar sabbin mambobi. Shi dai wannan tsari na MMM dole wanda yake ciki ya gayyaci wani kafin ya samu damar cin riba ko kuma mayar da kudin sa.

Su dai mambobin nada damar samun har Naira dubu talatin izuwa hamsin (N30,000 – N50,000) a karkashin tsarin na MMM.

Wani sashi na wasikar yana sanarwa da mambobi cewar “A cikin gasar, akwai masu nasara mutum hamsin. Na farko dai zai samu kudi Naira dubu dari biyar (N500,000), sai na biyu zai samu Naira dubu dari uku (N300,000) da kuma na uku zai tafi gida da Naira dubu dari biyu (N200,000).

Jaridar NAN ta ruwaito cewar a baya an gargadi al’umma da su guji shiga cikin tsarin MMM. A watan Diamba na 2016 tsarin ta samu nakaso bayan rufewa da suka yi daga fitar da kudaden wadanda suka shiga.

Sai dai a watan Janairu sun samu dawowa a ranar 13 inda daga yaba suka saka shingi na fitar da kudade wanda hakan ya jawo da dama suka fita daga cikin tsarin.

Asalin Labari:

NAN

1438total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.