Kamfanin Facebook ya bijiro don yin gogayya da gidajen talbijin

Katafaren shafin sada zumunta na Facebook ya sake yin wata hobbasa, inda ya bullo da fasahar bidiyo, da za ta yi gogayya da YouTube da kuma tasoshin Talbijin.

Nan gaba kadan masu amfani da Facebook za su ga sabon madannin Kallo, wanda zai ba su damar ganin shirye-shirye iri daban-daban, wasu daga ciki kamfanin ne ke daukar nauyinsu.

Madannin mai suna ‘Watch’ zai dace da bukatun mutum, ta yadda mai amfani da Facebook zai iya gano sabbin shirye-shirye, bisa la’akari kan abin da abokansa suke kallo.

Masu kallo za kuma su iya ganin sharhi da kuma haduwa da abokansu, har ma su hada wani rukunin abokai don kallace-kallace.

“Kallon wani nuni ba zai kasance, wani abu da ba hannun mai kallo ba,” a cewar mutumin da ya assasa kamfanin, Mark Zuckerberg a wani bayani da ya wallafa a Facebook.

“(Fasahar) ka iya ba da damar musayar wata gogayya da kuma tattaro mutanen da suka damu da wasu abubuwa waje guda.”

Tsawon wani lokaci Facebook yana da fasahar bidiyo a shafinsa, sai dai har zuwa yanzu, faya-fayen bidiyon da ba na kwararru ba, da kuma takaitattun shirye-shiryen kafofin yada labarai ne suka fi mamayewa.

A bara ne, katafaren kamfanin Facebook ya kara madannin bidiyo, inda kuma ya nuna cewa zai iya yin wani yunkuri don samar da shirye-shirye na ainihi.

Fasahar Kallo ta Facebook za ta iya bude sabuwar kofar samun kudin shiga ga kamfanin da kuma masu watsa shirye-shirye, yayin da masu kallo za su iya ganin tallace-tallace kafin da kuma a cikin wasu shirye-shirye da ake nunawa.

Karanta:  Snapchat tayi ragista da mahukunta a Rasha ba tare da sanin ta ba

Sharhin Leo Kelion, editan sashen Fasaha na BBC

Facebook ya ce yana fata fasahar shirye-shiryensa ta bidiyo za ta biya bukatun wani kebantaccen fannin rayuwa da kuma na daukaci.

Idan zabin da aka kaddamar wani abin misali ne, to fasahar za ta mayar da hankali kan shirye-shiryen nishadantarwa na rayuwar zahiri ciki har da girke-girke, da shirin tabbatar da koshin lafiya, da shirin tafiye-tafiye, wadanda za su fi dacewa a kan wayoyin zamani, maimakon shahararrun wasannin kwaikwaiyo da fina-finai wadanda masu tsadar shiryawa kuma sun fi dacewa da talbijin inda mai kallo zai iya yin waiwaye.

Cunkushewar kasuwa

Facebook na shiga kasuwar da take kara zama mai sarkakiya da cunkoso, inda za ta goga kafada da tasoshin talbijin na asali gami da shafukan bidiyo na intanet kamar YouTube da Netflix.

A ranar Laraba, kamfanin Disney ya ba da sanarwar cewa daga shekara ta 2019, zai fice daga yarjejeniyar da ya sa hannu da Netflix, inda zai bullo da fasahar yada shirye-shiryensa kai tsaye ga jama’a.

Zai kuma bullo da hanyar yada shirye-shiryen wasanni na ESPN shekara mai zuwa.

Tun tuni Facebook na da jerin shirye-shirye da suka hadar da gasar kwallon kwando a Amurka da gasar kwallon kwandon mata da shirye-shiryen kula da yara da wani shirin rayuwar namun daji daga National Geographic.

Fasahar ‘Watch’ za ta takaita ne a Amurka kafin ta fita ta kara bazuwa.

Asalin Labari:

BBC Hausa

809total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.