Kamfanin Kuli Kuli ya samu nasara a bajakolin Jihar Legas

Kamfanin First Class Refreshment ya kasance daya daga cikin kamfanonin da suka yi fice gami da samun nasara a bajakolin da aka gudanar a jihar Legas dake kudancin Najeriya.

Bajakolin wadda aka fara a ranar 2 ga watan Nuwanba zuwa yau Lahadi 11 ga watan na Nuwanba ta samu halartar manyan kamfanunuwa daga bangarorin nahiyoyi daban daban.

First Class Refreshment ya kasance mafi shahara a bangaren kayan abincin gargajiya da suka hada da Kuli-Kuli, Dambun Nawa, Kilishi, Bakilawa, Nakiya, Alkaki da dai sauran kayan abinci na al’adun kasar Hausa.

Shugaban kamfanin Badamasi S. Burji yayi wa Allah godiya daYa kawo su karshen wannan bajakoli inda ya yabawa dumbum masoya da sukayi cincirin do wajen sayen kayan kamfanin na First Class Refreshment.

A watan daya gabata ne dai kamfanin na First Class Refreshment ya samu nasara a bajakolin cinikayya ta Nigeria da kasar American da aka gudanar a birnin Abuja.

204total visits,1visits today


Karanta:  Malaman Jami’ar Bayero Sun Tallafawa ‘Yan Gudun Hijira

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.