Kamfanin zirga zirga na Firdausi zai fara jigilar maniyyata zuwa Hajj

Kamfanin zirga zirga na Firdausi mai hedikwata a jihar Kano da kuma rassa a wasu bangarori na arewacin Najeriya zai fara jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki a ranar Lahadi mai zuwa.

Shugaban kamfanin, Alhaji Aliyu Abdullahi Mai Ashana Jega shine ya sanar wa da wakilin Muryar Arewa a wata tattaunawa da suka yi a ofishin kamfanin dake shiyar Kano.

Alhaji Aliyu Abdullahi Mai Ashana Jega ya bayyana cewar Alhazan na su zasu tashi daga filin jirgin saman Mallam Aminu Kano dake garin Kano zuwa Madina dake kasar Saudi Arabiya a ranar Lahadin mai zuwa.

Ya kara da cewa kamfanin na Firdausi yayi wa Alhazan bana tanadin ingantatcen muhalli a kasa mai tsarki. Jega ya yi kira ga maniyyatan dasu kiyaye dokokin da aka shinfidawa maniyyata a gida Najeriya da kuma kasa mai tsarki. Kuma ya bukaci da su yiwa kasar su addu’a da shuwagabanni baki daya.

613total visits,1visits today


Karanta:  Buhari ya soki majalisar dinkin duniya kan 'yan gudun hijira

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.