Kano ta Tara Gudunmowar Biliyan 2 don Tallafawa Wadanda Annobar Gobara ta Shafa a Jihar

Ranar Lahdi (20/08/2017) ne gwamnatin jihar Kano ta jagoranci tara tallafin naira biliyan biyu don tallafawa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a jihar, tare da samun gudunmowa mafi girma ta Naira Miliyan 500 daga gurin shugaban taron, Alhaji Aliko Dangote.

Gwamnatin jihar ta shirya taron bada tallafin don taimakawa wadanda annobar gobara ta shafa a kasuwa sayar da waya (Farm Centre), kasuwar kurmi, da kasuwar singa da  kuma kasuwar Abubakar Rimi dake sabon gari.

Sauran waxanda suka bada gudunmowar sun haxa da bankin Access, wanda ya bada gudumowar Naira miliyan 100, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u wanda ya bada gudunmowar naira miliyan 50, bankin Ja’iz ya bada miliyan 10, bankin Zenith ya bada miliyan 20, kamfanin Skipa ya bada miliyan 10, Alhaji Xahiru Bara’u Mangal ya bada miliyan 25, yayin da gwamnatin Bauchi da ta Katsina suka bada miliyan 10 ko wannensu.

Shugabanin Riko na Kananan Hukumomi 44  suka bada gudunmowar naira miliyan 33.9, kamfanin gini na Brains and Hammers suka bada gudunmowar naira miliyan 20, Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Sarki ya bada miliyan 10, Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya bada miliyan 5, ‘Yan Majalisa Tarayya 24 da suka fito daga jihar suka bada gudunmowar naira miliyan 12

Shugaban taron, Alhaji Aliko Xangote yace ya zama wajibi su taimakawa wadanda annobar gobarar ta shafa “Kano ita ce ta farko idan ana maganar saye da sayarwa sannan jihar Legas” a cewarsa.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

703total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.