Karin Bayani Akan Harin Mubi

Yanzu an gano cewa dan kunar bakin wake ne yayi shigar burtu ya tada bam a cikin wani Masallaci garin Mubi

Masallacin da dan kunar bakin waken yakai har yau Talata ana kiransa Masallacin Madina a garin Mubi. Kafin a ankara dan kunar bakin waken ya tada bam din dake jikinsa yayinda mutane suke sallar asuba kuma kammala raka’a daya

Yawancin mazauna wurin ‘yan kabilar Shuwa ne da suka fito daga jihar Borno sanadiyar rikicin Boko Haram. Yawancin wadanda suke cikin Masallacin ‘yan Shuwa ne.

Wani ganao ya ce mutane da dama suka rasa rayukansu. Jami’an tsaro sun gallaza wurin suna taimakawa.

Shugaban karamar hukumar Mubi ta arewa Musa Ahmed Bello da aka fi sani da suna Ahmed Ajayi ya ce tuni aka garzaya da wadanda suka jika zuwa asibitin garin. Ya ce bisa ga yanayin gari ya kamata mutane suna kula. Su daina saurin mantuwa. Ya ce kawo yanzu mutane 15 zuwa 20 ne bam din ya kashe.

Asalin Labari:

VOA Hausa

727total visits,1visits today


Karanta:  Tsohon babban alkalin Najeriya Aloysious Katsina-Alu ya rasu

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.