Kasashen Duniya Na Dabda Sanya Hannu Don Haramta Nukiliya

Kasashen duniya 51 sun shirya tsaf don sanya hannun kan wata yarjejeniya da za ta haramta mallakar makamin Nukiliya a duniya, abin da Amurka da sauran kasashen da suka mallaki irin wannan makamin ke matukar adawa da shi.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da rikickin nukiliyar Koriya ta Arewa ke dada kamari, lura da yadda ta ke ci gaba da gwaje-gwajen makamin duk da takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba ma ta.

Kimanin kasashe 122 ne suka goyi bayan assasa dokar ta haramta mallakar makamin a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a cikin watan Julin da ya gabata bayan wasu jerin yarjejeniyoyi da kasashen Brazil da Mexico da Afrika ta Kudu da New Zealand suka jagoranta.

Sai dai kasashe 9 da suka hada da Amurka da Rasha da Birtaniya da China da Faransa da India da Pakistan da Koriya ta Arewa da Isra’ila duk sun ki shiga cikin wadannan yarjeniyoyi.

Wadannan kasashe dai sun mallaki makamin na nukiliya.

Kungiyar tsaro ta NATO ta yi tir da yarjejeniyar haramcin, in da ta ce, za ta iya haddasa wata fitina ta hanyar kawo rarrabuwar kawuna.

Tuni dai aka jinjina wa Sakatere Janar na MDD Antonio Guterres, lura da cewa, a lokacin shugabancinsa ne tun bayan shekaru 20, aka samu irin wannan yarjejniya ta kwance damarar kasashe.

Asalin Labari:

RFI Hausa

1107total visits,10visits today


Karanta:  Gwamnatin Myanmar Zata Takaita Zirga-Zirgar ‘Yan Gudun Hijirar Rohingya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.