Tarihin Kawu Sumaila

Kawu Sumaila

Suleiman AbdulRahaman wanda aka fi sani da Kawu Sumaila, wani fitaccen dan siyasa ne a jihar Kano daake Najeriya. An haifi Kawu Sumaila a ranar uku ga watan Maris na shekarar alif dari tara da sittin da takwas (3 March 1968) a garn Sumaila dake Jihar Kano.

Kawu Sumaila ya kasance babban mai taimakawa Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, a bangaren Majalisar Wakilai ta Kasa. Sannan yayi dan majalisar wakilai ta kasa na tsahon zagaye uku daga shekara ta dubu biyu da uku zuwa dubu biyu da sha biyar.

Rayuwar Kuruciya da Neman Ilimi
An haifi Kawu Sumaila a ranar Lahadi, uku ga watan Maris na shekarar alif dari tara da sittin da takwas (3 March 1968) a kauyen Sumaila dake cikin karamar hukumar Sumaila a jihar Kano Najeriya daga mahaifin sa Alhaji AbdulRahaman Tadu da kuma mahaifiyar sa Hajiya Maryam Muhammad.

Yayi makarantar firamare a garin na Sumaila a shekarar alif dari tara da saba’in da shida (1976), sai kuma sakandare a shekarar alif dari tara da tamanin da biyu (1982) duka dai a garin Sumaila. Daga bisani Kawu ya samu halartar halartar jami’ar Bayero dake Kano inda yayi karatun diploma a fannin ilimi. Kawu Sumaila yaci gaba da karatun sa da Degree a budaddiyar jami’ar Najeriya wanda aka fi sani da National Open University of Nigeria (NOUN).

Kawu yayi kwasakwasai da dama a kwalejoji da yawa wanda suka hada da Jami’ar Havard dake Amurka, sai Oxford dake kasar Birtaniya da kuma Cambridge duka dai a Birtaniya.

Rayuwar Siyasa
Kawu Sumaila ya shiga siyasa a shekarar alif dari tara da casa’in da daya inda ya zama dan jam’iyyar SDP a wancan lokaci. Kawu ya samu kansa a jam’iyyar PDM daga bisani wacce ta samu hadaka inda ta zama jam’iyyar PDP. Ya samu rike mukami na mataimaki a cikin jam’iyyar inda daga bisani ya tsaya takarar majalisar dokoki ta jihar Kano a shekarar alif dari tara da casa’in da biyar (1995) a karkashin jam’iyyar PDM da kuma alif dari tara da casa’in da tara (1999) a karkashin jam’iyyar PDP. A lokacin shirin mika mulki ga farar hula na zamanin gwamnatin marigayi Sani Abacha, Kawu Sumaila ya kasance mamba na jam’iyyar UNCP.

a shekara ta dubu biyu da uku (2003) ne Kawu Sumaila ya zama zababben dan majalisar wakilai ta kasa a karkashin jam’iyyar APP wanda ya samu kayar da takwaransa na jam’iyyar PDP Aliyu Kachako daga shiyar kananan hukumomin Sumaila da Takai. Kawu ya sake samun nasarar cin zabe zagaye na biyu a shekarar dubu biyu da bakwai (2007) da zagaye na uku a shekarar dubu biyu da sha uku (2013) duka bayan hadakar da jam’iyyar sa tayi inda ta samu komawa ANPP.

Kawu ya rike mukamai da dama a yayin zaman sa a majalisar wakilai wadanda suka hada da kwamitin yaki da talauci. A zagaye na biyu dana uku Kawu ya kasance mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar ta wakilai.

A shekarar dubu biyu da bakwai zuwa dubu biyu da sha daya (2007-2011) Kawu ya kasance mamba a kwamitin canza kundin tsarin mulki na kasa, sai kuma dubu biyu da sha daya izuwa dubu biyu da sha biyar (2011-2015) shima aka sake nada shi.

Takarar Gwamna
Kawu Sumaila ya kasance daya daga cikin jerin ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar Kano bayan kammala zagayen gwamna Rabiu Kwankwaso a shekarar dubu biyu da sha hudu (2014) a karkashin jam’iyyar APC. Daga bisani Kawu ya samu janyewa Abdullahi Umar Ganduje bayan an samu sasantuwa a tsakanin ‘yan takara.

Mukamai
Kawu Sumaila ya samu rike mukamai da dama a tsawon rayuwar wadanda suka fara daga matakin karamar hukuma,  jiha izuwa matakin kasa.

Kawu ya kasance babban mai taimakawa Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, a bangaren Majalisar Wakilai ta Kasa, mukamin daya fara a shekara ta dubu biyu da sha biyar (2015)

  1. Mamba na Kwamitin kawar da talauci ta Kasa shiyar Karamar Hukumar Sumaila
  2. Mamba na Dakin Ma’adanai ta Makarantun Jihar Kano
  3. Zababben Dan Majalisar Wakilai ta Kasa – Yuni 2003 zuwa Yuni 2007
  4. Zababben Dan Majalisar Wakilai ta Kasa – Yuni 2007 zuwa Yuni 2011
  5. Zababben Dan Majalisar Wakilai ta Kasa – Yuni 2011 zuwa Yuni 2015
  6. Mai Taimakawa Shugaban Kasa a Bangaren Majalisar Wakilai Yuli 2015 izuwa yanzu.

Sarauta da Lambar Girmamawa
Kawu Sumaila ya kasance mai rike da kambun Sarautar Gargajiya daga Karamar Hukumar Sumaila wanda aka nada shi a matsayin Turakin Sumaila karkashin jagorancin Dan Isan Kano kuma Hakimin Sumaila a shekarar dubu biyu da shida (2016).

A shekara ta dubu biyu da sha biyu shugaba Goodluck Jonathan ya dankawa Kawu Sumaila lambar girmamawa ta Kasa mai taken Order of the Federal Republic of Nigeria (OFR) a turance.

Shafukan Sada Zumunta
Twitter: Kawu Sumaila
Facebook: Kawu Sumaila
Wikipedia: Kawu Sumaila

1279total visits,1visits today