Kebbi ta Kashe Naira Miliyan 99 Wajen Biyan Tsofaffin Shugabanni

Gwamnatin Jihar Kebbi ta kashe kudi sama ga Naira Miliyan 99, domin biyan tsofaffin shugabannin kananan hukumomi 21dake fadin jihar.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta kashe kudi sama ga Naira Miliyan 99, domin biyan tsofaffin shugabannin kananan hukumomi 21dake fadin jihar. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin babban sakataren ma’aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu na Jihar Kebbi, Malam Sani Muhammed Yeldu, a lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa.

Malam Yeldu ya bayyana cewa tsofaffin shugabannin da suka amfana da wannan biyan sun hada da tsofaffin shugabannin da suka yi mulki tun daga shekarar 2004 zuwa 2008, wadanda suka samu kashi 30 cikin 100, a inda wadanda suka shugabanci kananan hukumomi daga shekarar 2014 zuwa 2015 suka samu kashi 40 cikin 100. Su ma tsofaffin shugabannin riko na 2014 zuwa 2015 na lokacin tsohon gwamna Saidu Dakingari sun samu nasu kaso cikin wannan biyan.

Baya ga wannan, ya bayyana cewa gwamnatin Jiha ta sake bayar da kimanin naira Miliyan 100, domin tallafawa malamman makarantun furamare 1,767 da makarantun Islamiyya da kuma ma’aikatun asibiticin karkara, in da ya jaddada cewa wannan bangaren za a kaddamar da shi nan bada jimawa ba.

A zantawarshi da jaridar aminiya, shugaban kungiyan tsofaffin kansiloli na Jihar Kebbi, Hon. Usman Ibrahim Maiyaki, ya godewa gwamnatin Jihar Kebbi bisa ga wannan namijin kokari da ta yi, kuma ya tabbatar da cewa an kafa kwamiti na musamman domin ganin cewa duk wanda keda hakki an biya.

Asalin Labari:

Aminiya

831total visits,46visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.