Kim Jong-un ya dakatar da kaiwa Amurka hari

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-un ya dakatar da kaiwa tsibirin Guam na kasar Amurka harin makami mai linzami a wata sanarwa da kamfanin labarai na Koriya din ya sanar.

Da yake jawabi akan haka, shugaban yace zasu dakatar da kai harin har sai sun ga motsin da Amurka zata iya yi kafin su dauki mataki.

A satin daya gabata ne dai Kim Jong-un ya bayyana cewar kasar sa zata kaiwa tsibirin na Guam harin makami mai linzami a wani yunkuri da ya tunzura shugaba Donald Trump.

Yunkurin kai harin dai ya tunzura shugaban Amurka Donald Trump inda yace kasar sa zata yaki Koriya ta Arewa muddin suka kai harin da suke ikirarin kaiwa.

A wani bangaren shugaban kasar Koriya ta Kudu, Moon Jae-in yayi kira ga dukkan bangarori dasu guji maganganun harzuka al’umma da juna baki daya. Ya kara da cewa kada Amurka ta kuskura ta kai takwarar ta ta Arewa ba tare da izinin kasar sa ba. Yayi bayanin babu wanda ya isa ya kai hari ba tare da amincewar kasar ba.

1554total visits,1visits today


Karanta:  Tillerson ya kai ziyarar tankwabe fada-a-jin Iran

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.