Kisan Musulmin Rohingya ya yi kama da kisan kiyashin Rwanda – Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nemi Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta dauki mataki kan musgunawar da ake yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

A jawabin da ya gabatar a babban taron Majalisar Dinkin Duniya na 72, Shugaba Buhari, ya ce irin abun da yake faruwa a Myanmar ya yi kama da irin kisan kiyashin da ya aka yi Bosniya a shekarar 1995 da kuma Rwanda a shekarar 1994.

Mutane a sassan duniya sun yi ta Allah-wadai kan irin musgunawa da ake yi wa Musulmi ‘yan kabilar Rohingya a Myanmar.

Shugaba Buhari ya kuma yi tsokaci kan matsalar Falasdinawa, inda ya nemi Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka musu wajen samar da kasa inda za su ci gashin kansu.

Ya ce a dukkan rikice-rikicen da ke faruwa, mata da yara ne suka fi fadawa cikin matsala.

Da yake tsokaci kan kasarsa Najeriya kuma, Shugaba Buhari ya ce kasar za ta ci gaba da goyon bayan MDD a duk wani kokarinta, wanda suka hada har da shirin samar da ci gaba mai dorewa a duniya nan da shekarar 2030.

“Tun lokacin da kasar ta shiga majalisar a shekarar 1960, Najeriya take ba da gudumawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya,” in ji Shugaba Buhari.

Asalin Labari:

BBC Hausa

927total visits,1visits today


Karanta:  'Majalisar dinkin duniya ta gaza hukunta dakarunta kan laifukan fyade'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.