Ko Liverpool za ta sayar da Coutinho?

Arsenal za ta iya sayar da dan wasan gaba, Alexis Sanchez, mai shekara 28, idan yarjejeniyar ta yi mata kyau, in babban wakilin Daily Mirror kan kwallon kafa, John Cross.

Tottenham ta kusa sayan dan Ajentina mai shekara 19, Juan Foyth daga Estudiantes kan kudi fam miliyan 8 kuma tana sake kokarin kammala cinikin Serge Aurier kan kudi fam miliyan 23, in ji Guardian.

Liverpool ta yarda ta sayar da dan wasan Brazil mai shekara 25, Philippe Coutinho, ga Barcelona a wata yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 148, in ji Yahoo Sports.

Duk da haka jagoran Liverpool, Peter Moore, ya nuna cewar ba za a sayar da Coutinho ba a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter kafin lokacin a rufe kasuwar ‘yan wasan ranar Alhamis, in ji Liverpool Echo.

Arsenal za ta iya sayar da dan wasan gaba, Alexis Sanchez, mai shekara 28, idan yarjejeniyar ta yi mata kyau, in babban wakilin Daily Mirror kan kwallon kafa, John Cross.

Inter Milan ta sake sabon tayi wa dan wasan gaban Arsenal mai shekara 25, Shkodran Mustafi, in ji Sky Sports.

Tottenham tana tunanin ko za ta jinkirta taya dan wasan tsakiyar Everton, Ross Barkley saboda matsalolin ciwon da dan shekara 23 din yake da su, in ji London Evening Standard.

Dan wasan West Brom na baya, mai shekara 29, Jonny Evans, zai ki komawa Arsenal saboda yana son komawa Manchester City, in ji Daily Mail.

‘Yan Baggies din sun shirya domin sayan dan wasan Poland mai shekara 27, Grzegorz Krychowiak daga Paris St-Germain, in ji Sun.

West Brom, za ta kammala sayan dan wasan bayan Arsenal Kieran Gibbs kan kudi fam miliyan 7 nan da sa’o’i 24, in ji Daily Mirror.

Dan wasan bayan Southampton Virgil van Dijk, mai shekara 26, yana da fatan komawa Liverpool, duk da cewar Arsenal da zakarun Firimiya Chelsea ka iya taya shi, in ji Independent.

Karanta:  Yadda 'yan kwallo Musulmai ke jure taka leda a lokacin azumi

Crystal Palace za ta goyi bayan kociya Frank de Boer da sayayya uku, in ji Daily Star.

Stoke City tana son sayan dan wasan tsakiyar Manchester City, Fabian Delph, mai shekara 27, kuma a shirye take ta taya dan wasan da aka saya daga Asoton Villa fam miliyan 8 , kan kudi fam fam miliyan 12, in ji Daily Telegraph.

Kociyan Newcastle United, Rafael Benítez, zai sayar da dan wasan gaba mai shekara 26, Dwight Gayle kan kudi fam miliyan 18, in ji Guardian.

Asalin Labari:

BBC Hausa

671total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.