Ko masarautar Saudiyya na da hannu a batan ‘ya’yanta?

Da sanyin wata safiya a ranar 12/06/2003, aka tasa keyar daya daga cikin Yariman wajen birnin Geneva.

Sunansa Sultan bin Turki yarima Abdulaziz bin Fahd, ya gayyace shi cin abincin safe.

Abdulaziz ya roki Sultan ya koma gida Saudiyya, inda ya shaida masa za a magance kace-nacen da ake yi kan sukar da ya ke yiwa shugabannin kasar.

Amma sai Sultan ya ki amincewa da hakan, a wannan lokacin ne yarima Abdul’aziz ya tashi daga inda suke zaune dauke da wayar salula da aka kira shi.

Jim kadan ministan harkokin addinin musulunci na Saudiyya Sheikh Saleh al-Sheikh da suke tare a dakin cin abincin shi ma ya fita, bayan dan lokaci sai wasu mutane sanye da wani bakin kyalle da suka rufe fuskokinsu da shi, su ka shigo dakin, suka kuma lakadawa Sultan dan karen duka, aka kuma soka ma sa wata allura a wuyansa.

Sultan ya shiga wani yanayi na dimuwa da gushewar hankali, a hakan aka dauke shi har filin jirgin sama na Geneva, aka sanya shi a cikin wani jirgi da daman ya na zaman jiran su ne.

Wannan labarin yarima Sultan ne ya shaidawa wata kotu a kasar Switzaland shekaru da dama da suka wuce.

Mai magana da yawun Sultan Eddie Ferreira na dakon dawowar maigidansa a Otal din da su ke zama a birnin Geneva, ya yi ta jiran dawowar uban gidan na sa amma shiru babu amo babu labari. Daga nan ne kuma labarin ya fara shan banban, a lokacin da suka kasa samun masu tsaron lafiyarsa, sun yi kokarin kiran wayar salularsa nan ma ta ki shiga.

”Da rana kuma sai labarin ya sha banban, don kuwa wasu mutane na daban ne suka kawo mana ziyara,” inji Mista Ferreira.

Ya kara da cewa ”Jakadan Saudiya a kasar Switzaland da manajan Otal din da mu ke, su ka shaida mana kowa ya yi ta kan sa. Saboda a cewarsa Yarima Sultan ya na birnin Riyadh domin haka ba a bukatar mu nan. Abinda zuciyata ta tambaye ni shi ne me Yarima ya yi da ‘yan uwansa suka masa duka tare da gusar ma sa da hankali da tasa keyarsa zuwa gida.”

Shekarun da suka gabata, da yariman ya zo duba lafiyarsa a kasar, ya yi Allwadai da dabi’ar take hakkin bil’adam da Saudiyya ke yi da kuma yadda cin hanci da rashawa ya yi katutu tsakanin ‘ya’yan masarautar da jimi’an gwamnati, ya kuma yi kiran ayi gagarumin garanbawul a masauratar.

Tun shekarar 1932, lokacin da sarki Abdulaziz da aka fi sani da Ibn Saud ya samar da kasar da a yanzu ake alfahari da ita a yankin gabas ta tsakiya ake tafiyar da ita a tsarin mulkin gargajiya da ba sa son wani ya kawo musu wargi.

Yarima Turki bin Bandar daya ne daga cikin manyan ‘yan sanda kasar mai mukamin Manjo, alhakin kula da masarautar na daya daga cikin ayyuka masu muhimmanci da ya ke yi.

Amma rikicin gado da ya taso a masarautar Saudiyya ya janyo masa zaman kaso, bayan fitowarsa daga Kurkuku sai ya yi gudun hijira zuwa kasar Faransa.

 

A shekarar 2012 ne ya fara wallafa bidiyo a shafin Youtube inda ta ke kiran a yi sauye-sauye a Saudiyyar.

Shi ma abin da ya faru da yarima Sultan ne ya kasance gare shi, inda hukumomin kasar sukai ta ma sa dadin bakin ya dawo gida, a kuma kan hakan ne mataimakin ministan cikin gida Ahmed al-Salem ya kira shi ta wayar tarho sai yariman ya nadi tattaunawarsu tare da wallafawa as hafukan sada zumunta.

A cikin tattaunawar al-Salem ya shaidawa Turki cewa ”Ko wa na farin ciki tare da zuba idon ganin ka dawo gida, Allah ya yi maka albarka.”

Karanta:  Majalisar Dokokin Jamus Ta Kai Ziyara Nijar Domin Tattaunawa Kan Harkokin Tsaro

Sai ya ce ”Su na zuba idon ganin na dawo gida? Ina maganar wasikun da ku ke aiko min? Inda ku ke rubuta kalaman batanci ciki har da kira na ”kai dan karuwa, sai mun tilasta maka dawowa gida kamar yadda mukai wa Sultan.”

”Ai babu wanda za mu bari ya taba ka, ka yarda dani ni dan uwan ka ne.”

” Wasikun da ake aiko min daga ofishin ka suke.” Dukkan tattaunawar da suka yi sai da Turk ya wallafa su a shafukan sada zumunta a shekarar 2015.

”Kusan ko wanne wata sai ya kira ni a waya ya na kokarin hillata ta na koma Saudiyya, daga baya kuma ban kara jin duriyar sa ba.” Inji wani abokinsa Wael al-Khalaf

Na shiga damuwa da kuma zargin wani abu ya faru da shi, daga bisani wata majiya daga wani babban jami’in Saudiyyata ta sanar da ni ai Turki ya na hannun masarautar, haka na nufin sun sace shi.

Na dauki lokaci mai tsaho ina son sanin halin da Turki ya ke ciki, sai daga bisani na ga wani rubutu da aka yi a wata jaridar kasar Morocco, ce wa Turki na kan hanyar dawowa Faransa bayan wata ziyara da ya kai Morcco, a lokacin aka kama shi aka kulle shi a gidan kaso. Bayanai sun nuna hukumomin Saudiyya ne suka tattauna da na Morroco suka bada izinin cafke shi da tasa keyar sa zuwa gida da amincewar wata koton kasar.

Ba dai mu san abin da ya faru ba da Turki bin Bandar ba, kafin bacewarsa ya bai wa abokinsa Wael wani littafi da ya rubuta a cikin littafin ya yi wani ruhutu mai kama da wahayi.

Inda ya rubuta ” Ya kai dan uwana Wael, ka adana wannan bayanin da zan bar maka har sai an sace ni ko an hallaka ni sannan ka bayyana shi ga duniya. Saboda na san za a sace ni ko ma su hallaka ni, na san yadda suka take min hakki da sauran ‘yan Saudiyya.”

Kusan lokaci guda da bacewar yarima Turki, wani yariman shi ma ya bace. Yarima Saud bin Saif al-Nasr – ya kasance mai matsakaicin ra’ayi, ya na kaunar yin wasan caca na Casino, ya na kuma kaunar zama a manyan Otal.

A shekarar 2014 shi ma Saud ya fara wallafa rubuce-rubucen da ya ke yi a shafukan twitter na nuna adawa da mulkin da ake yi a kasar sa.

In da ya ke kiran a gurfanar da manyan jami’an gwamnatin Saudiyya a gaban shari’a, wadanda suka mara baya aka hambarar da shugaban kasar Masar Muhammad Morsi a shekarun da suka wuce.

A watan Satumbar shekarar, abubuwan da Saud ke wallafawa suka kara zafafa.

Lamarin ya samo asali ne bayan wani yariman masarautar da ba a bayyana sunan sa ba, ya rubuta wasiku guda 2 ya na kira a hambarar da mulkin sarki Salman, ba tare da shawara ba kawai sai Saud ya danna alamun amincewa ya kuma zamo na farko a masarautar da ya aikata hakan. Hukuncin wanda ya aikata hakan tsattsaurai ne dan kuwa laifin cin amanakar kasa ne ya rataya akan shi.

Bayan wasu kwanaki, ya wallafa a shafinsa na twitter ”Ina kira ga al’uma su duba wasikun nan da idon basira, tara da matsa lambar ganin an aikata haka,” daga wannan rana ba a kara gani wani sako da ya wallafa ba.

Bayan Saud, sai kuma yarima Khaled bin Farhan, wanda ya yi hijira zuwa kasar Jamus a shekarar 2913- wanda ya yi amanna an yaudari Saud inda ya tashi daga Milan zuwa Rome dan ganawa da wasu abokan kasuwancinsu daga kasashen Rasha da Italiya da suke son bude reshen kamfaninsu a yankin Gulf.

Karanta:  Sa'udiyya Ta Bude Iyakokinta Ga Mahajjatan Qatar

An yaudare shi da hawa wani jirgi mai saukar ungulu daga Milan da nufin zai sauka a Rome amma bai tsaya ko ina ba sai a birnin Riyardh, kamar yadda yarima Khaled ya wallafa. Ya kara da cewa an hada baki ne da hukumar leken asirin Saudiya dan aiwatar da aikin.

”A halin da ake ciki baki daya yarima Turki da Saud na garkame a gidan kaso, gidan kason ma na karkashin kasa da babu wanda ya san da shi” inji Khaled.

Yarima Sultan, da akai masa daurin talala a Saudiyya na cikin mawuyacin hali, a farkon shekarar 2010 masarautar ta amince a fitar da shi kasar waje dan neman magani saboda tsananin ciwin da ya ke fama da shi, an kuma kai shi asibitin Boston, da ke Massachusetts.

Abin da ya yi wa masarautar a lokacin da ya ke kwance a asibitin Amurka, ya kuma shigar da karar masarautar a wata kotu da ke Switzerland, ya na zargin yarima Abdulaziz bin Fahd da Sheikh Saleh al-Sheikh da alhakin sace shi a shekarar 2003.

Lauyansa ba’amurke Clyde Bergstresser, ya karbo sakamakon binciken lafiyarsa da aka yi a asibitin sarki Faisal Specialist Hospital da ke Riyadh, inda aka kwantar da Sultan a ranar 13 ga watan Yulin 2003, sakamkon ya nuna an sanya masa wata siririyar roba a bakinsa dan taimaka mi shi yin nunfashi a lokacin da aka yi masa wata allura, sanadiyyar hakan wani bangare na jikin sa ya shanye.

Wannan shi ne karo na farko da wani dan masarautar Saudiyya ya gurfanar da wani gaban kotun kasashen yammacin duniya abin mamakin kuma ya shigar da karar ne kan daya daga cikin mutanen gidansu.

Sai dai lauya Bergstresser ya yi korafin gwamnatin Switzerland ta nuna halin ko in kula kan batun.

”Babu wani abun azo a gani da aka yi kan abin da ya faru a filin jirgin sama, ba a san su waye matuka jirgin ba? Shin me aka shirya jirgin zai yi a lokacin da ya sauka a kasar da kuma tashin sa zuwa Riyadh?

An sace yarima a kasar Switzerland, mutane za su yi tunanin ko hakan ya faru da sanin kasar da kuma amincewarta? Kai akwai tarin tambayoyi da ba mu da amsar su,” inji Lauya Bergstresser.

A watan junairun 2016, yarima Sultan na zaune ne a wani hamshakin Otal da ke birnin Paris, kamar dan uwan sa yarima Saud bin Saif al-Nasr a lokacin ne aka sace shi.

Ya na shirin kai wa mahaifinsa ziyara, wani Ba’masare da ya yi kaurin suna wajen sukar lamirin gwamnatin Saudiyya, a lokacin ne gwamnatin Saudiyya ta yi masa tayin za a kai shi a jirgi mai alfarma da kuma tayin za a duba lafiyarsa ta hanyar wani kwararren likita da masu tsaron lafiyarsa daga Amurka da tarayyar turai . Duk da ya san abin da ya same shi a shekarar 2003, sai ya amince da su.

Biyu daga cikin mutanen da akai komai kan idon su, sun bayyana yadda lamarin ya faru amma sun roki a sakaya sunan su saboda dalilai na tsaro.

“A lokacin da muka isa filin jirgi, sai muka ga wani babban jirgi a gaban mu, an rubuta sunan Saudiya baro-baro a jikinsa.”

Dayan kuma sai ya kara da cewa ”Ana iska sosai a lokacin da muka je, mun samu mutane da yawa a cikin jirgin kuma dukkansu maza ne.”

Jirgin ya tashi sama, da kuma aka nuna daga nan kasar Masar ya nufa kamar yadda kwamfuta ta nuna, amma bayan mun tashi sama da kamar sa’a biyu da rabi sai komai ya dakata ba ma gane inda muka nufa.”

Karanta:  An zargi Saudiyya da 'yada ta'addanci' a Birtaniya

Daya daga cikin tsaffin ma’aikatan shi ya ci gaba da bayyana cewa a lokacin da suka tashi yarima Sultan ya na bacci, ya tashi sa’a daya gabannin saukar jirgin, ya leka ta tagar ciki sai jikinsa ya fara bari.

A lokacin da matukin jirgin ya sanar da cewa za a sauka a kasar Saudiya, sai yariman ya fara ihu da buga kofa ya na kiran azo a taimaka ma sa, ma’aikatan yariman sun yunkuro za su je wurin sa sai ma’aikatan jirgin suka gargade su da su zauna a inda su ke.

Daya daga cikinsu ya ci gaba da cewa ”Da muka kalli waje ta tagar jirgin, sai muka ga dandazon mutane rike da manyan bindigogi, sun kewaye jirgin cikin shirin kar ta kwana.”

An dauke yariman da likitansa aka kai su wani kebantaccen gida, cike da matakan tsaro. Aka bar ma’aikatan yariman a cikin jirgin, daga bisani sai wasu mutanen na daban suka zo suka dauke su zuwa wani Otal. Sun kwashe kwanaki 3 ba tare da an ce musu uffan ba, babu fasfo ko wayar salula, daga bisani aka kawo musu kayansu tare da umartarsu su fice daga kasar zuwa duk inda suka so.

Daya daga cikin ma’aikatan yariman ya gane wani ma’aikacin jirgi, kuma shi ne ya ba su hakuri kan abin da ya faru ba tare da ya kara cewa komai ba.

”Abin da kawai ya shaida ma na shi ne, mun zo wurin da bai dace da mu ba, a kuma baudadden lokaci dan haka ya na kara ba mu hakuri kan abin da ya faru,” inji wani ma’aikacin yariman.

Shi ma dayan ma’akacin ya kara da cewa ”Ban amince da abin da ya faru gare ni ba, an sace ni, an kuma kawo ni kasar da ban sa ni ba, ba kuma tare da amincewa ta ba.”

Lamarin akwai firgitarwa, baya ga yarima Sultan, an sace wasu mutane 18 ‘yan kasashen waje, kuma hukumomin Saudi na da hannu a sace su, dan sojojin kasar ke tsare da su. Tun daga wannan lokacin ba a kara jin duriyar yarima Sultan ba.

Dan haka an bukaci gwamnatin Saudiyya ta maida martani kan zarge-zargen da ake ma ta amma har yanzu ba ta ce uffan ba.

A bangare guda kuma, yarima Khaled ya na can kasar Jamus inda ya yi gudun hijira, amma cike da fargaba da damuwar watakil abin da ya faru ga sauran ‘yan uwan sa zai zo gare shi.

”Mu hudu ne ‘yan uwan juna da muke zaune a kasashen turai, mu na adawa da yadda ake tafiyar da mulki a kasar mu da kuma masarautar mu ke jagora, an sace uku daga cikin mu, yanzu ni kadai na yi saura.” inji yarima Khaled.

Amma hakan na nufin shi ma ya na kan hanyar sacewar?

“Ina da tabbacin ba za su yi kuskuren aikata abin da suka yi wa sauran ‘yan uwa na ba, kuma mutane sun shaida min idan sun so yin haka ai da tuni ta faru. Sai dai ba na cikin walwala, ba na jin dadi, amma duk da hakan ‘yanci na ya na da matukar muhimmanci.”

1066total visits,4visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.