Korea Ta Arewa Tayi Gwajin Sabon Makami Mai Linzami

Makamin da Korea ta Arewan ta harba shi da sanyin safiyar yau, ya ketara ta saman tsibirin Hokkaido da ke arewacin kasar, kafin fadawa teku.

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, na cigaba da tattaunawa kan harba sabon makami mai linzamin da kasar Korea ta Arewa tayi a yau Talata, wanda a wannan karon ya ketara arewacin Japan kafin fadawa Teku. Lamarin da ake kallo tamkar tsokana ganin yadda gwajin ke zuwa a ranar da majalisar dinkin duniya ta ware don haramta gwajin Nukiliya ko Makami mai Linzami.

Makamin da Korea ta Arewan ta harba shi da sanyin safiyar yau, ya ketara ta saman tsibirin Hokkaido da ke arewacin kasar, kafin fadawa teku.

Wannan dais hi ne karo na farko da Kasar ke harba makami mai lizamin da ya ketara kasar Japan, daga cikin jerin gwaje-gwajen makamin da ta gudanar a baya-bayannan.

Ko da yake a shekarun 1998 da kuma 2009 korea ta Arewan ta taba harba manyan rokokin da suka ketara ta saman Japan, gwamnatin waccan lokacin ta kare matakin da cewa, anyi amfani da rokokin ne wajen aika tauraron dan adam zuwa sararin samaniya amma ba don dakon makamai ba.

da yake kare kasarsa a zauren majalisar dinkin duniya, jakadan Korea ta Arewan a majalisar Han Tae-Song, y ace matakin harba makami mai lizamin da ya ratsa sararin samaniyar Japan, martani ne kan atasyen sojin da Amurka ta ke gudanarwa tare da hadin gwiwar kawayenta da ke nahiyar.

Asalin Labari:

RFI Hausa

487total visits,1visits today


Karanta:  Mutanen Rohingya Ba ‘Yan Kasa Bane – Sojin Myanmar

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.