Koriya ta Arewa ‘za ta tsokane wa Amurka ido’

Koriya ta Arewa ta ci alwashin yin ramuwar gayya ga Amurka da kuma dandana mata kudarta, a kan sabon takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta saka a kan haramta mata shirin makami mai linzami.

Kamfanin dillancin labarai na Koriya Ta Arewa KCNA, ya ce, bakin mambobin MDD ya zo daya wajen sanya wa kasar takunkumin, inda suka ce abin da take yin keta dokoki ne.”

A wani bangaren kuma, Koriya Ta Kudu ta ce Koriya ta Arewa ta ki amincewa da damar fara tattaunawa, inda ta yi watsi da shi a matsayin ba da gaske ake ba.

Takunkumin zai taimaka wajen rage kudin shigar da Koriya ta Arewa ta ke samu.

Yin baki dayan da hukumar tsaron MDD ta yi ya biyo bayan gwajin makami da Koriya ta Arewa ta sha yi , wanda ya kara tashin hankali a yankin.

A wani martani da ta mayar da kakkausar murya a karon farko a ranar Litinin, Koriya ta Arewa ta tsaya kai da fata cewa za ta iya ci gaba da shirinta na makami mai linzami.

Wani jami’in Koriya ta Kudu ya shaida wa BBC cewa, Mr Ri ya ki amincewa da damar da takwaransa ya bayar ta tattaunawa.

Sakataren wajen Amurka  shi ma ya halacci taron kasashen, inda ya yi magana game da Koriya ta Arewa.

Ya kara da cewa, “babbar alamar da Koriya ta Arewa za ta ba mu ita ce, ta fara shirin tattaunawa a kan dakatar da kaddamar da gwajin da take yi”

A ranar Litinin ne shugaban Amurka Donald Trump, ya yi magana da takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in, ta wayar tarho game da alakar gabar tekun Koriya.

909total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.