Kotu Na Tsare Da Wani Mutum Saboda Yin Lalata Da Wani Karamin Yaro

Wata Kotun Majistire a Kano ranar Laraba tayi ummarnin tsare wani mutum mai shekaru 46 da haihuwa mai suna Kabiru Usman saboda zarginsa da akeyi da lalata da wani karamin yaro dan shekara 12.

Usman wanda mazaunin unguwar Dawakin Dakata ne dake Kano ana yi masa shari’a bisa laifi guda laifin saduwa da karamin yaro.

Babban Alkalin Kotun Majistirin, Muhammad Jibrin ya bada ummarni tsare wanda ake zargin ya kuma  daga shari’ar zuwa 26 ga watan Satumba don cigaba da sauraro.

Tunda fari, Mai Gabatar da Kara Pogu Lale ya fadawa kotun cewa wani mutum mai suna Yusuf Suleiman wanda keda adireshi daya da wanda ake zargin shi ne ya sanar da caji ofis din ‘yan sandan Zango faruwar lamarin ranar 15 ga watan Augusta.

Ya fada cewa a wannan rana, Usman ya yaudari karamin yaron mai shekaru 12 da haihuwa zuwa gidansa dake unguwar Dawakin Dakata inda ya aikata badalar da yaron.

lokacin da ake karantawa wanda ake zargin laifinsa ya musunta aikata laifin.

Mai gabatar da kara yace wannan laifin ya saba da sashi na 284 na Kundin laifuffuka

 

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

639total visits,1visits today


Karanta:  Yaushe Buhari Zai kori 'Kurayen' da ke Gwamnatinsa?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.