Kotu Ta Baiwa Ghana Damar Hako Mai a Kan Iyakarta ta Côte D’Ivoire

Kotun karkashin jagorancin alkali Boualem ta ce Ghana bata mamaye kan iyakar Cote ‘d Ivoire ba sakamakon aikin nata na tono danyen man, kamar yadda Cote d’ Ivoiren ke ikirari a baya.

Kotun warware rikice-rikice a tsakanin kasashen duniya da ke birnin Hamburg na kasar Jamus, ta yanke hukuncin mikawa Ghana damar ci gaba da aikin hako man fetur a yankin kan iyakarta da Ivory Coast, matakin da ya kawo karshen tsawon shekarun takun-saka tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin Tullow Oil da ke gudanar da aikin bincike da hako man fetur a yankin, ya bayyana cewa zai fara aiki gadan-gadan domin hako akalla ganga dubu 80 a kowace rana daga farkon shekara mai zuwa.

Kotun karkashin jagorancin alkali Boualem ta ce Ghana bata mamaye kan iyakar Cote ‘d Ivoire ba sakamakon aikin nata na tono danyen man, kamar yadda Cote d’ Ivoiren ke ikirari a baya.

An dai shafe akalla shekaru 10 ana takaddama tsakanin kasashen biyu, kan wanda ya mallaki yankin ruwan da arzikin danyen man dana Iskar gas ke shimfide a karkashinsa.

Asalin Labari:

RFI Hausa

568total visits,1visits today


Karanta:  Sa'udiyya Ta Bude Iyakokinta Ga Mahajjatan Qatar

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.