Kotu Ta Mallakawa Gwamnatin Najeriya Wasu Gidajen Mrs Madueke dake Legas

A Legas Alkali Chuka Obiozo ya mallakawa gwamnatin Najeriya wasu gidajen Mrs Madueke, tsohuwar ministar man fetur, dake wata unguwar masu hannu da shuni a jihar Legas kamar yadda hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa, wato EFCC ta bukata

 

 

 

 

 

 

 

Hukumar EFCC ce ta gabatar da kara a gaban kotun Chuka Obiozo inda ta gabatar da sheidu da suka tabbatar an sayi gidajen ne da kudaden gwamnati.

Gidajen suna tsibirin Banana Island ne, wata unguwa ta masu hannu da shuni a jihar Legas.

A ranar 19 ga watan Yulin bana ne dai ta gabatar da sheidun da ya sa Alkali Obiozo yanke hukumcin kwace gidajen. Amma kafin ya yi hakan ya umarci hukumar EFCC ta buga cigiyar wadanda suka mallaki gidajen cikin jaridu. Idan babu wanda ya fito ya nuna gidajen nashi ne to kotun zata baiwa gwamnati gidajen.

Jiya da alkalin ya zauna bayan da wa’adin ya cika babu wanda ya fito ya nuna gidajen mallakarsa ne.

Lauyan hukumar EFCC Ansale Ozioku ya shaidawa kotu cewa sakamakon gazawar wani ya fito ya bayyana kansa a matsayin wanda ya mallaki gidajen ya zama wajibi bisa tsarin doka a mallakawa gwamnati gidajen.

Shehun Malami Muhammad Lawal Yusufari ya bayyana abun da hukumcin ke nufi. Yace idan ana zargin wani da mallakar wasu kadarorin da aka saya da kudin gwamnati hukuma nada hurumin ta kai kara kotu domin a mallakawa gwamnati kadarorin.

Hukumar EFCC ta gabatar da sheidun da suka nuna yadda aka yi anfani da wasu kamfanoni da bankuna aka wawure kudin gwamnati. Wasu jami’an bankuna sun tabbatar cewa lallai sun karbo wasu kudade daga hannun ministar a gidanta dake Abuja a shekarar 2013.

Asalin Labari:

VOA Hausa

667total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.