Kotun Daukaka Kara Ta Ce Gwamnatin Jihar Katsina Nada Damar Tuhumar Tsohon Gwamnan Jihar, Shema

Kotun Daukaka Kara dake zamanta a Kaduna taki amincewa da karar da tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema ya shigar gabanta cewa ta dakatar ta cajin da gwamnatin Jihar Katsina keyi masa bisa dalilin cewa ba a bayyana masa takardun karar da ake yi masa ba.

Kotun ta yarda da cewa wanda ake zargi nada ‘yanci a bayyana masa takardun zargin da ake yi masa amma korafin na Shema bazai wadatarba saboda bai gabatar dashi akan lokaci ba tun kafin karar.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, na cajin Shema da wasu mutum uku a gaban mai Shari’a Maikaita Bako na Babbar kotun Jihar kan zargin wawure kudin jihar naira biliyan 11 lokacin da yayi na tsahon shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar.

Shema yaje kotun ne inda yake bukatar a dakatar da cajin da ake yi masa a Babbar Kotun Jihar Katsina bisa dalilin cewa ba a bashi damar kare kansa ba.

Tsohon gwamnan sauda dama a baya ta hannun lauyansa JB Daudu ya musanta cewa ba a bashi damar tuntuba da ganawa ba kan wasu ayyukan da zasu taimaka wajen jin ta bakin kowa kan zargin da ake yi masa

Ya fadawa kotun cewa tuhumar da ake yi masa a kotun jihar da ramuwar gayya da zalunci wanda zata iya tauye masa ‘yancinsa inda ya bukaci Babbar Kotun data yi watsi da karar da Kotun Jihar ta Katsina keyi masa.

Da yake karanta hukuncin da kotun ta zartar Mai Shari’a H.A Abiru, cewa yayi kotun ta goyi bayan hukunci da Kotun Jihar Katsina ta zartar kan damar da Babban Mai Shari’ar Jihar Katsina keda shi na ummartar hukumar EFCC data binciki tsohon gwamnan.

Karanta:  Ba Wanda Zai Cire Magu - Osinbanjo

Sheman dai ya garzaya Kotun Daukaka Karan ne ranar 25 ga watan Mayu na shekarar 2017 da korafin kalubalantar zargin cin hancin da Babbar Kotun Jihar Katsina keyi masa.

Sai dai kotun daukaka karar ta zartar cewa babu wani abun da ya sabawa kundin tsarin mulki kan hukuncin babbar kotun jihar Katsinan na kyale Gwamnatin Jihar bawa hukumar EFCC ummarnin bincikar tsohon gwamnan bisa zargin laifuffukan da ake yi masa.

Lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan yanke hukunci, lauyan Shema, Elisha Y. Kora cewa yayi suna da damar kin amincewa da hukuncin, zasu bayyana matakin da zasu dauka idan sun sami  kwafin takardun hukuncin inda zasu yi musu duba na hakika.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

1138total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.