Kotun ICC Ta Yanke Hukuncin Diyyar Tumbuktu

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta zartas da hukuncin biyan diyyar Yuro milyan 2 da digo 7 na barnar da Mayakan Mali suka tafka a birnin Tumbuktu mai dogon tarihi sakamakon rushe kaburburan manyan Shehunnai a shekarar 2012.

Tun a watan Satumbar bara ne dai kotun ta yankewa mutumin daya jagoranci lalata Kaburburan Shehunnan Ahmad al-Faqi al-Mahdi hukuncin daurin shekaru 9 a gidan yari, sai dai a hukuncin da alkalin ya yanke yau, ya ce ya ragewa asusun amintattu na masu laifi su yanke nawa ya kamata ya biya.

Tun a shekarar 2004 ne dai aka samar da asusun wanda ke da nufin magance matsalolin mutanen da suka fuskanci tuhume-tuhumen manyan laifuka ko laifukan yaki.

Ana yiwa garin Tumbuktu lakabin birni mai shehunai 333, saboda manyan malaman da aka birne a garin.

Tarihi ya nuna cewa Abzinawa ne suka kafa garin a karni na 12, kuma a karni na 15 da 16 garin ya shahara wajen koyar da addinin Islama, inda mutane suka dinga zuwa daga wurare masu nisan domin samun ilimi.

Haka kuma kayakin tarihin garin na karkashin kulawar asusun ilmi kimiyya da al’adu na majalisar dinkin duniya.

Kuma a shekarar 2012 ne mayakan suka rushe dukkanin kaburburan tare da lalata muhimman abubuwan tarihin dake birnin na Tumbuktu.

Asalin Labari:

RFI Hausa

411total visits,1visits today


Karanta:  'Cigaban Afirka ne Kawai Zai Magance Matsalar Bakin-Haure'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.