Kotun Koli ta Kenya ta rushe zaben Shugaban Kasa

Kotun Koli a kasar Kenya ta rushe zaben da aka gudanar a kasar Kenya wanda shugaba Uhuru Kenyatta ya lashe inda ta umarci da a sake gabatar da sabon zabe nan da kwanaki 60 masu zuwa.

Rushe zaben dai ya biyo bayan korafin da bangaren ‘yan adawa ya shigar karkashin jagorancin Raila Odinga wanda ya sha kaye a zaben da aka sanar a kasar a watan daya gaba ta.

Alkalai hudu cikin shida ne suka zabi a rushe zaben bayan korafin da Mista Odinga ya shigar wa da kotun bayan yayi da’awar cewar a zabga magudi a zaben.

“An gudanar da zaben shugaban Kasa ba bisa ka’idar kundin tsarin mulki ba, don haka zaben ya kasance rusasshe” inji alkali David Maraga bayan bayar da umarnin sake zabe a kwanaki 60.

Mista Odinga na cike da murna bayan rushewar zaben. “Wannan wata rana ce mai cike da dunbin tarihi ga al’ummar Kenya dama Afrika baki daya” Inji Mista Odinga.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, CNN

3000total visits,1visits today


Karanta:  Zaben Kenya: Sakamakon farko ya nuna Kenyatta ya sha gaban Odinga

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.