Kungiya Ta Dauki Nauyin Almajarai 300 Karatun Boko

Wata kungiya mai Kokarin ilmantar da Almajjirai karatun boko da shirye-shiryen kawar da talauci (Mass Almajiri Literacy and Poverty Alleviation Initiative) ta dauki nauyin daukar dawainiyar almajirai 300 karatun boko a Kebbi.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya rawaito cewa matar gwamnan Kebbi, Hajiya Aisha Bagudu ce ta kafa kungiyar a shekarar 2009 da zimmar rage adadin yawan yaran da basa zuwa makaranta dama manyan da suka girma basuyi karatu ba a jihar.

Wannan kungiya, kungiyace da bata gwamnati ba ta dauki dawainiyar yara sama da 300 zuwa

Shugaban kungiyar a kasa bakidaya, Mr  Mceba Temofe shi ya bayyanawa manema labarai haka a Birnin Kebbi ranar Alhamis.

Temofe yace kungiyar ta samar da yanayin karatu mai kyau a cibiyoyinta dake cikin jihar don kokarin samar da ilimi ga yaran da suka cancanci shiga makaranta.

A cewarsa, samada yara 300 ne yanzu haka aka dauki dawainiyarsu zuwa makaranta, 26 daga ciki yara mata ne sai 14 manyan mata.

“Kungiyar na aiki ka’in da na’in don samar da gurin koyon karatu mai kyau da yara zasu samu ilimi a kusa dama rungumar yaran da basu da damar samun ilimin,” a cewarsa.

Shugaban kungiyar na kasa yace kungiyar na tuntubar hukumomin gwamnatin jihohi, gwamnatin tarayya, kungiyoyin duniya dana cikin gida don yin aiki tare da niyar habaka rayuwar yara marasa gata ta hanyar basu ilimi.

“Yanzu haka wannan kungiya mai suna MALPAI a takaice ita take dauka dawainiyar kanta, muna dorawa mambobinmu nauyaye-nauyaye haka kuma muna neman tallafi don ganin mun sami taimako,” a cewarsa.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

461total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.