Kungiyar Boko Haram Ta Sake Salon Kai Hari

Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa yanzu haka mayakan Boko Haram sun sauya salo inda suke fakewa yin zaman makoki domin kai hari kamar yadda suka yiwa mutanen Madagali garin dake kusa da dajin Sambisa inda suka ja tunga.

 

 

 

 

 

Wannan ne dai kusan karo na uku a kasa da mako guda da yan kungiyar ta Boko Haram suka kai hari a wasu kauyuka na yankin Madagalin dake daura da dajin Sambisa.

Yayin wannan harin ,kamar yadda rahotanni ke cewa yan tada kayar bayan sun yi shigar burtu ne a kauyen Bakin Dutse a wani yanayi na masu makoki,da hakan ya jawo hankalin jama’a zuwa inda suke wanda kuma nan take suka soma bude wuta ba kakkautawa.

Kawo yanzu hukumomin tsaro basu yi karin haske ba tukunna game da wannan sabon harin.

To sai dai dan majalisar wakilai mai wakiltar Madagali da Michika, Mr Adamu Kamale,ya tabbatar da faruwan lamarin,inda ya bukaci da a kara tura sojoji zuwa wasu yankunan dake kusa da dajin na Sambisa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da wa’adin da babban hafsan sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya dibarwa dakarun sojin kasar na su kamo Imam Abubakar Shekau dake zama shugaban wani bangaren na kungiyar Boko Haram ke kara karadowa,batun da masana harkar tsaro ke ganin akwai abun dubawa.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1195total visits,2visits today


Karanta:  "An yi wa Fulani kisan-ƙare-dangi a Taraba"

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.