Kungiyar “Concerned Nigerians” Ta Ce Shugaba Buhari Ya Dawo Kan Aiki Ko a Tsige Shi

Wata kungiya mai rajin kare demokuradiyya a Najeriya da ake kira “group of concerned Nigerians”, ta yi kira ga majalisar ministoci data dokokin tarayya su gaggauta kafa komiti da zai tantance lafiyar shugaba Muhammadu Buhari ganin ya kusa cika kwanaki 90 baya kasar.

Shugaba Buhari dai tun a farko farkon watan Mayu ne ya tafi Ingila domin jinya, kodashike a baya bayan nan jami’an kasar wadanda suka ziyarce shi a birnin London, sun ce shugaban ya sami sauki, yanzu umarnin likita ne yake dako.

Shugaban kungiyar ta Concerned Nigerians, Deji Adeyanju, ya gayawa Saleh Shehu Ashaka cewa kungiyar sa zata tafi majalisa ind a zata bukaci majalisar dattijai ta kafa kwamiti kamar yadda tsarin mulki ya tanada domin tantance ko shugaba Buhari yana karfin ci gaba d aaikinsa.

Gameda tasirin wannan mataki ganin shugaban ya mika iko ga mataimakinsa Parfessa Yemi Osinbanjo, Deji yace, shirme ne kawai, har yanzu hadiman Buhari ne suke rike da madafun iko kuma ahalin yanzu komi ya tsaya a cik a kasar.

Kan mataki na gaba da zasu dauka, idan majalisa bata biya musu bukata ba, Deji, yace daga shugaban kasa har zuwa ‘yan majalisa, talakawa suka zabe su, saboda haka tilas ne su yi abunda ‘yan kasa suke so.

Asalin Labari:

VOA Hausa

536total visits,1visits today


Karanta:  Zan Yaki 'Yan Ta'adda da Miyagu – Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.