Kungiyar Kananan Hukumomi A Najeriya Ta Nace Sai A Bata ‘Yancin cin Gashin Kai.

Kungiyar maaikatan kanan hukumomi sun gudanar da 'yan kware-kwaren zanga-zanga zuwa majilisar dokokin jihar Niger domin neman majilisar tasa hannu a dokar da zata basu damar cin gashin kai

Ma’aikatan kananan hukumomi Najeriya naci gaba da fafitukar ganin sai an basu ‘yancin cin gashin kansu.

Shugabanin kungiyar kananan hukumomin suka ce sun jima suna fuskantan karancin kudaden da zasu gudanar da ayyukan ci gaba a yankunan su.

Sukace hakan ko ya samo asalli sakamakon asusun hadin gwiwar da suke da ita tsakanin su da gwamnatocin jihohin Najeriya .

Daya daga cikin shugabannin kungiyar ta kasa Komrade Abdullahi Aliyu da ya jagoranci ma’aikatar kananan hukumomi zuwa majilisar dokokin jihar Niger ya shidawa wakili sashen Hausa Mustafa Nasir Batsari cewa.

‘’Dalilin mu na zuwa majilisar dokokin jihar Niger shine akan maganar cin ‘yancin gashin kai na kananan hukumomin da muke neman majilisun dokokin jihohi su sa muna hannu, kamar yadda majalisar dokokin ta kasa ta amince da wannan dokar, shi yasa muke bi jiha-jiha domin suma suyi yadda takwarorin aikin su na tarayya suka yi’’.

Asalin Labari:

VOA Hausa

337total visits,1visits today


Karanta:  'Yansandan Najeriya Sun Kama Masu Sace Mutane Tsakanin Kaduna da Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.