Kungiyar Kwadago Ta Ce Ta Na Bin Jihar Kano Biliyan 33

Bayanai daga jihar Kano na cewa kungiyar kwadagon jihar ta ce mambobinta na bin hukumomi makudan kudaden fansho da sauran hakkokin ma'aikata.

Kungiyar kwadago ta kasa a Najeriya reshen jihar kano, ta ce ta na bin gwamnatin jihar kano bashin sama da Naira bilyan 33, a zaman kudin fansho da hakkin ma’aikata.

Saboda haka ne kungiyar kwadagon take tuni ga gwamnatin jihar da ta saka batun ma’aikata a sahun farko idan ta fara kasafta kudaden da ta samu daga hanun gwamnatin tarayya, wani kaso na biyan basussuka da jihohin na Najeriya suka karba, daga kasashen yammaci, sama da da abinda ya kamata su biya.

Wannan karon, jihar ta sami sama da Naira biliyan dubu 10.

Shugaban kungiyar kwadagon a jihar kano Comrade Kabiru Ado Minjibir ya ce ya koka kan yadda kusan ba’a la’akkari da wadanda suka jima suna dakon kudaden fanshon su.

Da yake magana kan wannan batu, kwamishinan kudi na jihar Farfessa Kabir Isa Dandago, ya yi alkawarin cewa jihar za ta mutunta sharuddan da gwamnatin tarayya ta shimfida game da yadda za su yi amfani da kudaden.

Wannan karo, gwamnatin tarayya ta na son su ware kashi 75% cikin dari na kudaden wajen biyan bukatun ma’aikata.

Asalin Labari:

VOA Hausa

851total visits,1visits today


Karanta:  'Yan majalisar dokokin Kano 6 sun sauya sheka

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.