Kungiyar Tuntubar Juna Ta Dattijan Arewa (ACF) Tayi Maraba Da Janye Ummarnin Da Aka Bawa ‘Yan Kabilar Igbo Na Ficewa Daga Yankin

Kungiyar Tuntubar Juna ta Dattijan Arewa tayi maraba da matakin da Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa suka dauka na janye ummarnin da suka bawa  ‘yan kabilar Igbo mazauna arewa ficewa daga yankin ranar 1 ga watan Oktoba. Inda kungiyar ke cewa “Wannan wani cigaba ne mai kyau da zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da cigaban kasa dama dorewar Nijeria a matsayin kasa guda”.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Jumma’a, mai Magana da yawun kungiyar, Muhammad Ibrahim Biu yayi nuni da cewa matakin yayi dai-dai da matsayar da suka dauka tun da fari cewa “tsarin dimokaradiyyar wanda damfare yake da bin doka da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya bada dammar kai-komo cikin fadin kasarnan ga duk Dan Kasa domin neman abinci ba tare da tsangwama ba.

A ta bakinsa, Kungiyar Dittijan ta Arewa ta “yaba kokarin Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa da Alhaji Kashim Shettima da wasu shugabannin arewa.

“Kungiyar ta yaba kokarin farko da Mataimakin Shugaban Kasa, Furofesa Yemi Osinbajo yayi na jawo hankalin Jagororin Arewa, Sarakunan Gargajiya da shugabannin kabilar Igbo wajen kawar da rudanin da Masu neman kafa kasar Biyafara da ayyukansu suka haifar da kuma ummarnin ficewa daga arewa da Samarin Arewa suka bawa ‘yan kabilar Igbon.

Sanarwar ta rufe da cewa “Dattijan na Arewa sun roki daukacin ‘yan Nijeriya dasu kula korai da manufofin Gwamnatin Tarraya na kawar da dukkan kalaman batanci da duk wani yinkuri na haifar da hatsaniya a kasa wadda zata rusa zaman lafiyar kasa dama kasantuwar Nijeriya a matsayin kasa guda”

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

2234total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.