Kwale-kwale ya yi Ajalin Mutum 12 a Lagos

Mutum 12 sun halaka a lokacin wani hatsarin kwale-kwale dauke da fasinja a Legas ranar Lahadi, a cewar gwamnatin jihar, wadda ta dora alhakin hatsarin a kan daukar mutane fiye da kima a cikin jirgin.

Hukumar da ke kula da hanyoyin sufurin ruwa ta jihar Legas ce ta sanar da aukuwar hatsarin, inda ta ce an gano karin gawa uku, lamarin da ya sanya adadin mutanen da suka mutu zuwa 12.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato hukumar tana cewa an kai mutum hudu asibiti kuma suna ci gaba da samun kulawar likita.

Hatsarin ya auku ne a kusa da unguwar Ilashe da ke gabar teku.

Gwamnatin Lagos ta kuma ce rashin bin doka na daga cikin dalilan da suka janyo aukuwar hatsarin.

“Wani hatsari, wanda abin takaici ne ya faru a Ilashe… saboda yadda aka makare jirgin ruwan da fasinjoji a jirgin dakon ayaba daga wata tashar fasa-kwauri”, in ji sanarwar da hukumar ta fitar.

Har yanzu hukumomi ba su iya tantance yawan fasinjojin da ke cikin jirgin ba, amma gwamnati ta ce ayarin masu ceto na can na yunkurin gano ko akwai sauran wasu da suka nutse a cikin teku.

Asalin Labari:

BBC Hausa

662total visits,1visits today


Karanta:  Dawowar Buhari ta karo karfin gwuiwa - Gwamna Bello

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.