kwamanda na Boko Haram ya mika wuya a Jihar Borno

Sojojin sunce a na bincikan kwamandan na Boko Haram har ya furta gaskiya cewa yana daya daga cikin wadanda suka kai hari jihar Adamawa a garin Madagali da kuma sauran jihohi na arewa ta gabas inda suka kashe matasa da yawa.

Daya daga cikin manyan Kwamandoji na Boko Haram mai suna Auwal Isma’il ya mika wuya ga sojojin Najeriya da suke aiki a yankin jihar Borno.
 
Isma’il ya sanar da jami’an tsaron cewar shi babban ma’aikaci ne a kungiyar ta Boko Haram inda ya taka babbar rawa, ya kara da cewa yana daya daga cikin wadanda suka kai samame a a makarantar ‘yan mata ta Chibok a shekara ta 2014 inda sukayi awon gaba da yara sama da 300.
 
Sojojin sunce a na bincikan kwamandan na Boko Haram har ya furta gaskiya cewa yana daya daga cikin wadanda suka kai hari jihar Adamawa a garin Madagali da kuma sauran jihohi na arewa ta gabas inda suka kashe matasa da yawa.
 
Ya kuma ce in sha Allah zai taya jami’an tsaro, ya kuma basu bayanai masu muhimmanci sannan zai sanar dasu inda maboyar sauran kwamandojin kungiyar suke
Asalin Labari:

Muryar Arewa

1088total visits,1visits today

Karanta:  Kashe Nnamdi Kanu sojin Nigeria suka zo yi - Bar Ejiofor

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.