Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Hada Wata Tawaga Ta Kwararru Don Suyi Bincike Kan Fadan Da Ya Faru Ranar Hawan Daushe

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Mr Rabi’u Yusuf, ya kaddamar da wata tawaga ta kwararrun ‘yan sanda don suyi bincike kan fadan da aka gwabza ranar Asabar tsakanin dariku biyu na Jam’iyyar APC a cikin birnin Kano.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, DSP Magaji Majiya ne ya sanar da hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Kano ranar Jumma’a.

Yace tawagar ta hada da Matemakin Kwamishinan ‘Yan sanda Mai Kula da Sashin Bincike kan Manyan Laifuffuka, Mr Ahmed Muhammad Azare, wanda aka dorawa alhakin gano musabbabin fadan da ya faru ranar 2 ga watan na Satumba.

A cewarsa, an baiwa tawagar masu binciken ummarnin gano wadanda suka kawo harin da wandanda harin ya rutsa dasu da wanda suka dauki nauyi da kuma shirya harin da kuma gano cewa ko akwai hannun ‘yan sanda gun kai harin ko akasin haka.

Ya kuma tabbatar da cewa za a tsare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Yayi kira ga mutanen jihar da su bawa yan sanda hadin kai wajen gano wadanda suka shirya wannan mummunan aikin.

Majiyan kuma yayi watsi da korafin ‘Yan Kwankwasiyya cewa sun so magana da Kwamishinan ‘Yan Sanda amma yaki yarda ya gana dasu.

“Abin takaici ne cewa wasu mutane na son haifar da rudani kawai don son shafawa ‘yan sandan da suka tseratar da rayuwarsu kashin kaji,” a cewarsa.

Ya kuma ce babu wata furofaganda ko matsi ko fadin abun da bai faru ba ko kaucewa gaskiya da zata hana rundunar ‘yan sandan aikinsu na kare doka da oda.

“Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya bazata bar wata kungiya ko wasu mutane ta kowacce siga su ruguza zaman lafiyar da ‘yan kasa ke ciki yanzu haka ba.

Karanta:  Jihar Jigawa Ta Gudanar Da Zabe Duk Da Kotu Ta Hana

“Rundunar ‘Yan Sanda na gargadin duk wani mai son haifar da yamutsi ta kowacce hanya cewa bazasu saki jiki suna kallon ‘yan daba na cin karensu ba babbaka ba a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya tuna cewa mutane da dama ne suka samu munanan raunuka lokacin fadan da aka gwabza a Harabar Fadar Mai Martaba Sarki tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan jihar Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso dana Abdullahi Ganduje

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

827total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.