Kwankwaso ya Kauracewa Babban Taron APC a Kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bai halarci babban taron jam’iyyar APC na jihar wanda aka gudanar jiya.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bai halarci babban taron jam’iyyar APC na jihar wanda aka gudanar jiya.
Sai dai kuma sanatoci biyu daga jihar wadansu suka hada da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da ke wakiltar Kano ta Kudu da Sanata Barau Jibril da ke wakiltar Kano ta Arewa sun halarci taron wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha karkashin tsauraran matakan tsaro.
Alhaji Abdullahi Abbas wanda yake tafiyar da al’amuran jam’iyyar a matsayin shugaban na wucin gadi ya zama cikakken shugaban jam’iyyar na jiha.
Kafin fara zaben, Wakilin Jam’iyyar na Kasa, Prince Nwoko Orinze, ya ce sun zo jihar ne don tabbatar da an gudanar da zaben jam’iyyar bisa ka’ida.
“Jam’iyyar ta shirya zaben ne don a cike guraben mukaman jam’iyyar”. Inji shi
A jawabinsa, Shugaban Kwamitin Tantance ’Yan takara, Muhammad Nadu Yahaya ya bayyana cewa duk wadanda suka halarci zaben sun cancanci su kasance a wurin.
Ya ce sai da kwamitin ya bi ka’idojin da jam’iyyar ta gindaya na tantance ’yantakara  kafin su gabatar da sunayensu.
To amma bangaren jam’iyyar wanda Umar Haruna Doguwa ke yi wa jagoranci ya yi watsi da taron inda ya bayyana shi da “Taron Jeka-na-yika”.
Doguwa ya shaida wa Aminiya cewa “Abin da bangaren Abdullahi Abbas ya yi ba komai ba ne illa taron Jeka-na-yika saboda shugabancin jam’iyyar na kasa bai bayar da umarnin wani ya gudanar da babban taro na jiha ba”.
Asalin Labari:

Aminiya

2539total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.