Kwankwaso yana nan daram a jam’iyyar APC

Sakataren kwamitin APC na tattaunawa shiyar jihar Kano, Suraju Kwankwaso yayi Allah wadai da rahotanni da suke ta watsuwa kan cewar Sanata Kwankwaso ya koma jam’iyyar adawa ta PDP.

Surajo Kwankwaso yayi nuni da cewar wadannan jita jita ne kawai, sannan wani lamari ne da bashi da tushe ko kadan.

A wata waya da jaridar Punch tayi da shi yace Kwankwaso cikakken dan jam’iyyar APC ne, sannan bashi da wani kuduri na fita daga cikin jam’iyya.

Sai dai ya bayyana cewar taron gaggawa yana gudana domin kawar da jita jitar ta barin jam’iyyar APC.

Surajo Kwankwaso yace hasali ma uwar jam’iyya ta kasa babu wanda ta aminta dashi illa bangaren Sanata Rabiu Kwankwaso a jagorancin jam’iyya na jihar Kano.

Asalin Labari:

Muryar Arewa da Punch

1216total visits,1visits today


Karanta:  Lokacin Sauya Fasalin Najeriya Ya Yi - IBB

One Response to "Kwankwaso yana nan daram a jam’iyyar APC"

  1. IDRIS TELA GILIMA   August 15, 2017 at 3:51 pm

    lo bai radio yau ba, musa mass rana gone,don jamiyar APC tamkar zaman agolanci ne,inga takura said lows ya lima guidance su.

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.