Liverpool Ta Yarda Su Cigaba Da Tattaunawa Da Barcelona Akan Cinikin Coutinho

Masu Kulub din Liverpool Fenway Sports Group sun yarda su cigaba da tattaunawa da kulub din Bacelona kan yiyuwar sayar da Philippe Coutinho

Shugaban kulub din Liverpool tun da fari a farkon watan nan ya fitar da wata sanarwa dake nuna cewa dan wasan nasu bana sayarwa bane.

Sai dai wata majiyar yada labarai dake Spain ta nuna cewa tattaunawa da wakilan na Coutinho ya kayatar yanzu zasu iya saurar farashin na Barca

Tuni dai kulub din na Liverpool dake Anfield yayi watsi da farashin da Barca ta bayar akan dan wasan har sau uku

An dai ce abin da ya ragewa Liverpool shi ne su nemi wanda zai maye gurbin dan wasan tun kafin su sallama shi akan farashin da yayi kusa da £148m.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

815total visits,1visits today


Karanta:  Mai horas da ‘yan kwallon Kamaru yace ‘yan wasansa sunfi na Najeriya gogewa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.