‘Ma’aikata da dama bulus suke ci saboda rashin iya aiki’

Shugaban Hukumar kula da cigaban fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA, Dr. Isa Ali Pantami ya ce ma fi yawancin ma’aikatan ba su cancanci albashi da suke ci ba.

A wata hira da BBC kan irin aikace-aikace da kalubalen da ma’aikatarsa take fuskanta, Dr. Pantami ya ce “Za ka ga ma’aikata 500 amma bai fi mutum 50 ne suke iya yin aikin da aka dauke su su yi ba.”

Ya kara da cewa ” Wani idan ka ba shi ya rubuta maka takarda ta minti daya lokacin da za ka dauka wajen gyara rubutun ka kwammace da kanka ka rubuta.”

Dr. Pantami ya bayyana kwararrun ma’aikata wadanda za su iya duk abin da aka umarce su da yi da wadanda za su iya taimaka ayyuka sun tafi dai-dai.

Wannan matsalar dai da sauran matsaloli kamar rashin wadatattun kudade da ma’aikatar tasa ke fuskanta, ya bayyana su da abubuwan da ke ci wa hukumar tasa tuwo a kwarya.

Najeriya dai na da ma’aikatan gwamnatin tarayya kusan dubu dari.

Dr. Isa Ali Pantami ya ce ya yi amanna cewa nan gaba, ci gaban kasashen duniya zai ta’allaka ne akan karfin bangaren fasahar zamaninsu, amma ba ga albarkatun karkashin kasa ba.

Ya ce ya zama wajibi ga kasashe masu tasowa irin su Najeriya, su dora fifiko ga bunkasa fasahohi a cikin gida, muddin suna so a tafi tare dasu a duniya.

Sai dai kuma Dr Pantami ya kara da cewa hukumarsu ta dukufa wajen magance asarar kudade da Najeriya ke yi yayin shigo da kayayyakin fasaha daga waje.

Asalin Labari:

BBC Hausa

2808total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.