Macron Ya Mara Baya Ga Masu Kyamar Wariya A Amurka

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana goyon bayansa ga masu kyamar wariyar launin fata na kasar Amurka. Shugaban cikin wani sako ta shafin Twitter daya wallafa a yau karara ya nuna goyon bayansa ga masu akidar yaki da wariyar launin fatar.

Cikin sakon da shugaban na Faransa Emmnuel Macron ya aike ya nesanta kansa  daga mara baya ga masu akidar kyamar launin fata, lamarin da kuma yazo dai-dai da bukatar da ake da ita ga mutane musamman shugabanni.

Wannan sako dai bai fito fili ya kushe Shugaban Amurkan Donald Trump ba, wanda ke ci gaba da fuskantar chachchaka a dan tsakanin nan saboda irin kalaman da suka rika fitowa daga bakinsa, bayan wani al’amari daya faru a Charlotsville na Jihar Virginia a Amurka.

Ministan waje na kasar Jamus Sigmar Gabriel ya fadi cewa shugaban Amurka Donald Trump ya tafka kuskure saboda kin fitowa fili ya la’anci abinda ya faru a kasarsa na nuna waiyar launin fata.

Tarzoma dai ta barke ne a wajen wani gangami a Charlotville saboda yunkurin tuge wani tsohon Kwamandan sojan Amurka wanda ya taka rawar gani wajen hada kan kasar Janar Robert Lee wanda yam utu shekaru 147 da suka gabata.

Asalin Labari:

RFI Hausa

813total visits,1visits today


Karanta:  Amurka za ta sayar wa Nigeria jiragen yaki

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.