‘Maganar Fatar Baki Ba Za Ta Magance Matsalar Tsaro Ba’

Mukaddashin Shugaban Najeriya ya ce lokaci ya yi da mahukuntan kasar za su aiwatar da matakan shawo kan kalubalen tsaro daban-daban da suka tunkaro kasar a halin yanzu a maimakon maganar fatar baki.

Farfesa Yemi Osinbajo na magana ne yayin wani muhimin taro da dukkanin gwamnoni da shugabannin hukumomin tsaron kasar da aka kira taron koli kan tsaro da tattalin arziki; wanda aka yi a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Daya daga cikin gwamnonin Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, wanda ya yi wa manema labarai karin bayani kan abubuwan da suka tattauna, ya ce taro ne na tsaro na kasa da aka fadada shi daga taron da aka saba yi na tattalin arzikin kasa.

Ya kuma ce su gwamnonin sun bayyana abubuwan da suka dame su na tsaro a yankunansu.

” Manyan abubuwan da suka fi damun mu sune matsalar masu satar shanu, da satar mutane domin neman kudin fansa, da hare-haren Boko Haram, da na masu neman a raba kasa da makamantansu”.

Gwamna Ganduje ya kuma ce duk an tattauna kan wadannan batutuwan kuma an amince cewa su jami’an tsaro za su zauna a tsakaninsu su tattauna abubuwan sosai su kuma ba da haske kan yadda za a shawo kan wadannan matsaloli.

An kuma cimma wata matsaya a taron cewa za a dau matakan tuntubar juna tsakanin jami’an tsaro da masu mulki, kana su kan su al’ummar kasar akwai rawar da ake bukata su rika taka wa wajen samar da bayanan abubuwan da ke faruwa a yankunansu, wanda ta hakan ne zai taimaka wajen yakar bata-gari da matsaloli na tsaro daban-daban a kasar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

710total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.