Magoya Bayan Shaikh El-Zakzaky Sun Yi Gangamin Neman Sako Jakoransu

Yan kungiyar Shiya masu goyon bayan jagoransu Shaikh Yakubu El-Zakzaky sun yi gangamin neman a sakoshi da matarsa a birnin Yola babban birnin jihar Adamawa

Su dai magoya bayan El-Zakzakin sun gudanar da jerin gwanon ne har zuwa ofishin hukumar kare hakkin dan adam ta Najeriya,wato Human Rights Commission dake Yola wanda ke kula da jihohin Adamawa da Taraba inda suka samu tarba daga jami’an hukumar.

Yayin dai wannan zanga-zangar lumanar hukumar kare hakkin bil Adam ta Najeriyan, Human Rights Commission ta yi alkawarin tilasta gwamnatin Najeriya sake jagoran kungiyar ‘yanuwa Musulmi Sheikh Ibrahim El-Zakzaky dake tsare tun cikin watan Disambar shekarar 2015. Mr Ebel Jingi,jami’in hukumar ya bayyana haka ga almajiran Malamin yayin wannan zanga-zangar inda ko ya shawarci mabiya Al Zakzakin da su zama masu bin doka da oda.

Abubakar Abdul Mumini da ya jagoranci wannan jerin gwanon yace sun ziyarci ofishin hukumar ne domin mika kukansu ga hukumar game da cigaba da tsare Malaminsu da gwamnatin kasar keyi.

Mata ma dai ba’a barsu a baya ba, yayin wannan jerin gwanon inda suka bayyana ra’ayoyinsu da cewa:

A ranar 2 ga watan Disamba na shekarar 2016, wata babban kotu dake Abuja karkashin jagorancin Justice Gabriel Kolawole ta bada umarnin a saki El-Zakzakin shi da matarsa Malama Zeenat. Amma gwamnati ta yi watsi da umurnin inda ta ci gaba da tsare El-Zakzaky da matarsa batun dake cigaba da jawo suka daga kungiyoyi na ciki da wajen Najeriya.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1198total visits,2visits today


Karanta:  Rashin Hanyoyi Ya Hana Kaddamar da Tashar Jirgin Ruwa Ta Kan Tudu a Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.