Mahajjaciya Ta Rasa Ranta A Makka

Wata Mahajjaciya daga karamar hukumar Igala-mela ta jihar Kogi, mai suna Hajiya Asma’u Iyawo Abdullahi ta rasu sakamakon rashin lafiya yayin da take gudanar da aikin hajji a Makka.

Shugaban Hukumar Alhazan, jihar Sheik Lukman Abdullahi Imam ne ya sanar da cewa Mahajjaciyar ta rasu ranar Talata da safe yayin da yake karin haske kan aikin Hajji a garin na Makka.

“Ta rasu bayan duk kokari da ma’aikatan lafiyar mu sukayi yaci tira. Dattijiwa ce wadda daga zuwanta kasa mai tsarki rashin lafiyar tata ya tashi. Muna addu’ar Allah ya jikanta ya kuma gafarta mata zunubanta, tuni dai aka binneta a garin na Makka.

“Banda wannan Mahajjaciyar da ta rasu, dukkanin Mahajjatanmu suna cikin koshin lafiya. Muna godiya ga Allah da yasa duk Mahajjatanmu cikin koshin lafiya”, a cewarsa.

Sheik Imam ya yabawa Mahajjatan jihar kan yadda suke gudanar da ayyukansu, da kuma bada hadin kai ga hukumar tasu.

2607total visits,1visits today


Karanta:  An saki wanda ya sanya wa karensa suna Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.