Mai horas da ‘yan kwallon Kamaru yace ‘yan wasansa sunfi na Najeriya gogewa

Uyo- Mai Horas da ‘Yan Kwallon Kamaru, Mr Hugo Broos, yace ‘yan wasansa wadanda ake kira da suna Indomitable Lions sunyi wasan zakaru na nahiyoyi a kasar Rasha don haka sunfi na Kasar Nijeriya da ake kira da suna Super Eagles gogewa.

Broos din ya fadi haka ranar Alhamis a wani taron manema labarai a garin Uyo a shirin da kasar Kamarun keyi na karawa da Nijeria ranar Jumma’a don neman gurbi a gasar kwallon duniyar da za ayi  a shekarar 2018

Mai horas da ‘yan wasan yace bayan kasar Kamarun ce Gwarzuwar Nahiyar Afrika a kwallon kafa sun kuma yi wasa da manyan kasashe kamar su Chile, Germany da Australia a Gasar Zakarun Nahiyoyi.

“Najeria na gaba damu da maki hudu, mun san cewa idan mukayi rashin nasara tamu ta kare. Don haka zamuyi wasa cikin kwarewa

“Kowa yasan sakamakon wasan gobe da na ranar Litinin na da mutukar muhinmanci, bana fargaba,” a cewar Broos din.

Yake cewa yaji dadin yanayin garin Uyo don haka zai buga wasan don samun nasara.
Kaftin din ‘yan wasa Kamarun Benjamin Moukandjo, cewa yayi sunyi shiri na sosai don tunkarar wasan.

Moukandjo ya goyi bayan mai horaswar tasu cewa wasan na gobe da kasar Nijeria ba karamin wasa bane.

“Na san cewa wasan gobe nada mutukar muhinmanci, idan har mukayi nasarar wasan burinmu na nan a raye na zuwa kasar Russia,” a cewarsa

Ya kuma ce kungiyarsu tuni sun shiryawa ‘Yan Kungiyar Super Eagles din. (NAN)

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

337total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.