Maigirma Alkali Tabbas Ni Mai Laifi Ne, Inji Evans

Daga Lagos- Kasurgumin Mai Satar Mutanen nan Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka fi sani da suna Evans da ake tsare dashi kan laifuffukan da suka hada da makirci da kuma satar mutane don neman kudin fansa ya bayyana a gaban Babbar Kotun Jihar Lagos dake Ikeja ranar Laraba ya kuma amsa laifuffukan da ake zarginsa dasu.

An dai kama Evans tare da wasu mutane biyar da suka hada da Uche Amadi, Ogechi Uchechukwu, Okwuchukwu Nwachuckwu, Chilaka Ifeanyi da Victor Chukwunonso Aduba.

Ana tsare dasu kan laifuffuka guda 2 wadanda suka hada da shirya makirci da kuma satar mutane don neman kudin fansa, jihar Lagos ce dai ke karar wanda ake zargin. Shi dai Evans da wanda ake kara na biyu da na hudu tuni suka amsa laifunsu, shi kuwa wanda ake kara na uku da na shida kin yarda sukayi da laifin da ake zarginsu da shi.

Jihar Lagos da ta shigar da karar ta hannun Antoni Janar da Kwamishnan Shari’a Adeniji Kazeem a bayanin karar da suka shigar sun bayyana cewa masu laifin sun aikata laifin tsakanin 12 ga watan Fabrairu da 14 watan Afirilun shekarar 2017.

Yace lamarin ya faru da misalin karfe 7:45 na yamma kan titin Obokun, Ilupeju dake Lagos.

Ya kara da cewa ranar 12 ga watan Afrilu Evans tare da sauran mutanen biyar dauke da bundigu da wasu muggan makamai suka sace tare da tsare da kuma karbar kudin fansa har zunzurutun kudi Euro 223,000 don sakin wani mai suna Duru Donatus.

A ta cewar mai gabatar da kara wannan laifin na karkashi manyan laifuka jihar Lagos sashi na 411 da 271 (3).

Karanta:  Ina samun sauki sosai — Shugaba Muhammadu Buhari

Lokacin da ake karanta musu laifin su Evans da wanda ake zargi na biyu da na hudu sun yarda da laifinsu

Ita kuwa ta ukun mace ce da na bayar da na shidan kin amincewa sukayi da laifin da ake tuhumarsu dasu.

Evans din cewa yayi “Maigirma Alkali ni mai laifi ne.”

Gama sauraren kare keda wuya, Dan Sanda mai gabatar da kara ya roki mai shari’a Hakeem Oshodi ya tsare wadanda ake zargin a gidan maza.

Inda yace “Zamu cigaba da rokon a tsare su don daga karar wadanda suka ki amincewa da laifin nasu, mu dawo da hojjoji kwarara da zasu taimaka a zartar da hukunci akan wandanda suka yadda da nasu laifin”.

Wanda ke kare mai lafi na farko da na biyu da na biyar cewa yayi ba zasu ja da daga karar ba.

Sai yanzu ne masu kariyar suka samu damar ganawa da wanda suke karewa da safen nan. Haka kuma yanzu aka gabatar musu da takardun karar na uku kuma basu samu damar ganawa da wadanda suke karewar ba don suna tsare a wajen ‘Yan sanda, don haka zamu so a daga karar don ganawa da wadanda muke karewa.

“kafin zama na gaba mun gama ganawa da wadanda muke karewa don wannan ba karamin laifi bane”.

Kafin mai shari’a Oshodi ya daga karar ya tambayi Dan Sanda mai gabatar da karar kurkukun da yake so akai masu laifin inda yace ya zabi a kaisu Kurkukun Kirikiri.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

349total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.