Tarihin Dr. Yusuf Maitama Sule (Dan Masanin Kano)

Alhaji Dr. Yusuf Maitama Sule wanda aka fi sani da suna “Dan Masanin Kano” wani shahararren dan siyasa ne a Najeriya kuma basarake wanda yayi fice a fanin difilomasiya. Dan Masani ya kasance dattijon kwarai har izuwa lokacin rasuwar sa a ranar 2 ga watan Yuli na shekara ta dubu biyu da sha bakawai.

An haifi Dan Masani a birnin Kano, na Jihar Kano a Najeriya a ranar daya ga watan Oktoba na shekara ta alif dari tara da ashirin da tara (1 October 1929). Ya yi rayuwar sa kusan gaba daya a birnin na Kano tare da iyalan sa. Sai dai har izuwa shekara ta alif dari tara da tamanin da uku (1983) ya kasance fitacce wajen rikon mukamai daban-daban a kasar Najeriya dama ketare baki daya.

Aiki
Dr. Yusuf Maitama Sule ya kasance hazikin gaske wanda aka sani da gaskiya gami da rikon amana. A lokutan rayuwar sa ta duniya Dan Masani ya kasance abin kwatance wajen yaki da cin hanci da rashawa. Wannan ce ma ta sanya aka nada shi mukamin Minista na Gyaran Kasa a lokacin da aka sake zaben Shugaban Kasa Shehu Shagari a karagar mulki kashi na biyu a shekara ta alif dari tara da tamanin da uku (1983), mukamin da aka nada shi domin taimakawa Shugaban Kasa yaki da cin hanci da rashawa.

Dan Masanin Kano ya rike mukamai a fannoni daban-daban kama daga zababbe izuwa nadadde. A shekara ta alif dari tara da hamsin da hudu (1954) ya rike mukamin bulaliyar majalisa a Majalisar Wakilai ta Kasa bayan zabar sa da akayi a matsayin wakili daga Arewacin Najeriya shiyar Kano. A shekarar alif dari tara da hamsin da shida (1956) kuma ya rike mukamin ministan wutar lantarki, sai kuma ministan Gyaran Kasa.

Dan Masanin Kano ya samu rike mukamin Kwamishinan Hukumar Korafe-Korafe ta Kasa a shekarar alif dari tara da saba’in da shida (1976). Sai jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya a shekarar alif dari tara da saba’in da tara (1979) inda anan ne ya rike mukami na musamman a matsayin shugaban kwamitin yaki da mulkin mallaka na Majalisar Dinkin Duniya a shekarar alif dari tara da tamanin da biyu (1982).

Rasuwa
Dr. Maitama Sule Dan Masanin Kano ya rasu a ranar biyu ga watan Yuli na shekara ta dubu biyu da bakwai (2 July 2017) a birnin Alkahira na Kasar Masar bayan ya sha fama da wata ‘yar gajeriyar rashin lafiya. An binne Maitama Sule a garin Kano inda aka yi masa Sallar Jana’iza a kofar gidan Sarkin Kano dake Kofar Kudu a ranar uku ga watan Yuli na shekara ta dubu biyu da bakwai (3 July 2017).

2123total visits,2visits today


3 Responses to "Tarihin Dr. Yusuf Maitama Sule (Dan Masanin Kano)"

 1. Zubairu Dalhatu Malami   July 17, 2017 at 6:25 pm

  Allah Ya jikan sa kuma yayi masa rahama Ya sa ya huta duniya da Lahira, amin.

  Reply
 2. Mustapha Musa Taudai   July 17, 2017 at 9:07 pm

  Add your comment Allah Yajikansa Yakuma Gafartamasa Zunubansa Yakuma Maidamana Da Irinsa A Arewa

  Reply
 3. shafiu Abubakar dogo   August 18, 2017 at 10:11 am

  Allah yajikansa da rahama kuma allah ya ba iyalansa hakuri

  Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.