Majalisar Dattawan Najeriya Ta Gamsu da Yadda Hukumar EFCC Ke Yin Aikinta

Majalisar Dattawan Najeriya, wadda ta ki ta amincewa shugaban riko na hukumar EFCC kujerar shugabancin hukumar, ta ce ta gamsu da yadda hukumar din ke gudanar da aikinta

Majalisar Dattawan Najeriya ta ce ta gamsu da yadda hukumar yaki da masu bata dukiyar kasar ko EFCC ke tafiyar da aikinta a yanzu.

A can baya an yi ta kai ruwa rana tsakanin majalisar da fadar shugaban kasa a kan shugaban riko na hukumar Ibrahim Magu.

Sanata Mustapha Sani Muhammad mai wakiltar kudancin jihar Neja kazalika mataimakin shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na majalisar dattawan yana mai cewa shugaban riko na hukumar ta EFCC Ibrahim Magu yana kokari.

Ya cigaba da cewa “mu kuma muna baya mun sa masa ido muna kallon cewa an yi kom a ka’ida”

Dangane da cewa majalisar ba ta shiri da Magu sai Sanata Sani Muhammad yace “a’a ba wai ba ma shiri da shi ba ne. Gwamnatin APC ce gaba daya. A cikin Senate majority ‘ya’yan APC ne. Gwamnatin Baba Buhari APC ne. Baba Buhari ya sa Magu a wurin. So, babu yadda za’a ce ba ma shiri”

A cewar Sanata din akwai banbancin fahimtar tsarin mulkin kasa domin wai su a Majalisa suna bin tsarin mulki bisa doka. Ya sake jaddawa “ba fada”.

A kan cewa sun dage sai an cire Ibrahim Magu, Sanata Muhammad ya ce ba haka ba ne. Yace mutane suna anfani da siyasa ne. Injishi yadda da doka ta ce shi za’a bi kuma shi suke bi.Ya kare da cewa basa fada da kowa.

Asalin Labari:

VOA Hausa

539total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.